'Yan Shi'a sun sanyawa tutocin kasar Amurka da ta Isra'ila wuta a Abuja
- 'Yan kungiyar 'yan uwa musulmai wato 'yan shi'a sun gabatar da zanga zanga jiya a Abuja
- Sun kone tutocin kasashen Amurka da Isra'ila a kokarin da suke na ganin an daina kashe musulmai a kasar Falasdinu
Jiya Juma'a ne 'yan kungiyar 'yan uwa musulmai wadanda aka fi sani da 'yan shi'a suka kone tutar kasar Amurka da ta kasar Isra'ila a lokacin da suke zanga-zanga akan kashe musulmai da ake yi a kasar Falasdinu.
Zanga-zangar wacce suka fara ta daga babban masallacin juma'a na Abuja, 'yan sanda sun tare su a daidai shatale-talen Julius Berger.
A lokacin kuma suka fara ihu suna kiran 'Free Zakzaky' 'Free Palastine', sannan suka tsaya a kasan wata gada inda dinga daga tutar Amurka da ta Isra'ilan daga baya kuma suka sanya mata musu wuta.
Lamarin ya kawo hatsaniya sosai a cikin birnin Abuja, inda hakan yayi sanadiyyar hada cunkoso na ababen hawa. 'Yan kungiyar suna zanga-zangar ne da bukatar a sakar musu shugaban su, Sheikh Ibrahim Zakzaky, wanda yake tsare a hannun hukuma tun watan Disambar shekarar 2015
KU KAARANATA: An so shugaba Buhari ya cire ni daga minista, saboda ana tunanin ni dan kungiyar asiri ne - Dalung
Ba wannan ne karo na farko da aka saba rikici da 'yan shi'ar ba, tun bayan lokacin da sojoji suka kama jagoran nasu a gidansa dake Zari'a a shekarar 2015.
Sau da dama 'yan shi'ar sukan hada gangami na zanga-zanga akan a sakar musu shugaban nasu, duk kuwa da irin kokarin da hukumomin tsaro suke na ganin sun kawo karshen zanga-zangar da suke yi din, wanda sanadiyyar ta akan samu asarar rayuka da dama ko kuma asarar dukiya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
Asali: Legit.ng