Yan sanda sun gano kokon kan wani magidanci a cikin motarsa

Yan sanda sun gano kokon kan wani magidanci a cikin motarsa

Mun samu labarin wani mumunan al’amari da ya afku da wani magidanci mai suna Malam Muhammad Saba, a ranar Jumaá karshe kafin a fara azumin Ramadana na wannan shekarar ta 2019.

Malam Saba dai na zaune ne a unguwar second gate da ke garin Suleja a jihar Niger kuma ya kasance dan asalin garin Bida duk a jihar.

Abunda ya faru kuwa shine a wannan rana Saba ya fita daga gidansa amma abun bakin ciki sai kokon kansa aka dawo wa iyalinsa dashi wanda aka tsinta a cikin motarsa.

Jami’an yan sanda ne suka gano kokon kan nasa a cikin motarsa da ya fita da ita.

Kafin rasuwarsa marigayin ya kasance ma’aikaci ne a sashin tattara bayanan filaye da taswirarsu na Abuja (AGIS).

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa ta tura wakilinta zuwa gidan marigayin amma ya tarar da gidan a rufe inda makwabta suka sanar da shi cewa an wuce da iyalan zuwa gidan iyayen marigayin da ke garinsu na Bida bayan zaman makoki a ranakun farko na aukuwar lamarin.

Aminiya ta zanta da wani makwabcin marigayin mai suna Malam Ndana Muhammad, inda ya ce ko a ranar ta Juma’a ya halarci Sallar Juma’a da kuma ta La’asar tare da marigayin, kafin washe gari ’yan sanda suka zo gidansa da labarin abin da ya faru, kasancewarsa makwabci ga marigayin.

“Bayan nan sun dauke ni zuwa babban ofishinsu na A dibision don in tantance ko shi ne, inda suka fito da kokon kansa daga cikin wani buhu, da suka ce sun gano a bayan motarsa bayan sun yi kicibis da wanda ake zargi da hannu a kisan, yana tuka motar marigayin sannan suka tsayar da shi bai tsaya ba,” inji shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda ta jihar, DSP Muhammad Dan-Inna wanda ya fitar da sanarwa a ranar Asabar da ta gabata, ya bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Samuel, wanda ya bayyana shi a matsayin aboki a gare shi.

Ya yi bayanin cewa motar sintiri ta ’yan sanda ta yi kokarin tsaida mutumin da ke tuka motar marigayin samfurin Toyota Camry tare da wasu a kusa da Garin Lambata da ke kan hanyar Suleja zuwa Minna, amma sai wadanda aka tsayar din suka yi harbi ga bangaren ’yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Aiki kawai: Gwamna Zulum yayi umurnin biyan bashin albashi da fansho ba tare da bata lokaci ba

Yan sandan sun mayar da martani, inda suka samu nasarar harbe Samuel a kafa sannan bayan sun bincika motar sai suka gano kokon kan marigayin a ciki.

A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya kashe marigayin tare da jefar da gangar jikinsa a wani waje a Jihar Nassarawa. Daga bisani wanda ake zargin ya mutu a Asibitin Suleja, inda aka garzaya da shi.

Tuni dai aka yi jana’iza tare da binne kokon kan marigayin a makabartan Suleja tun a ranar ta Asabar, kamar yadda wasu makusantan marigayin suka tabbatar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel