Yadda wayar salula ta yi sanadiyyar mutuwar wani saurayi

Yadda wayar salula ta yi sanadiyyar mutuwar wani saurayi

- Wayar salula ta yi sanadiyyar mutuwar wani saurayi a kasar Thailand

- An iske gawar saurayin ne a kwance a kan gado yayin da wayar tashi take caji a kusa dashi

Wani mutumi dan shekaru 22 a duniya daga kasar Thailand ya rasa ransa sanadiyyar wayar salula da ya sanya caji a kan gadon ya kuma kwanta bacci.

A cewar jaridar Dailymail, mutumin wanda ba a bayyana sunansa ba yana zaune shi daya ne a cikin dakin nashi inda yake jiran sauran 'yan uwanshi su karaso garin da yake mai suna Nakhon Ratchasima ranar Litinin da dare. A lokacin da 'yan uwan nashi suka zo dakin nashi, sun iske gawar shi ga kuma wayar tashi nan kusa dashi tana makale a jikin abin cajin.

Yadda wayar salula ta yi sanadiyyar mutuwar wani saurayi

Yadda wayar salula ta yi sanadiyyar mutuwar wani saurayi
Source: Facebook

Mutuwar mutumin ta zo watanni kadan bayan wani ma'aikacin kamfani shima wayar tayi sanadiyyar kashe shi a lokacin da ya sanya ta caji kuma yake amfani da abin jin kida na kunne a lokaci daya a kasar Thailand din. An samu gawar Kritsada Supol a kan gadonsa da wayarsa jone a jikin wuta a watan Fabrairun wannan shekarar.

KU KARANTA: Wata mata ta bayyana yadda ta yi mutuwar karya yayin da 'yan bindiga suka kashe duka danginta a jihar Filato

Mai gidan da yake haya yaje dakin marigayin da safiyar ranar da lamarin ya faru inda ya iske gawar shi kwance akan gado da alamar konewa a kunnensa. Haka ya nuna cewa yana jin kida ne ko kuma waya da wani lokacin da lamarin ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel