Ku bari ayi ma yaranku rigakafin shan inna – Inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Ku bari ayi ma yaranku rigakafin shan inna – Inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauhi yayi kira ga iyaye dasu dinga bari ana yi ma yayansu rigakafinr yaki da cutar shan inna don samar da yara masu cikakken koshin lafiya a kasa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malamin ya bayyana haka ne yayin taron rufe tafsirin Al-Qur’ani na watan Ramadana daya gudana a dandalin Murtala dake cikin garin Kaduna, a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Sabon gwamna ya kara mata ta 3 kwana daya bayan darewarsa madafan iko

Ku bari ayi ma yaranku allurar shan inna – Inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Ku bari ayi ma yaranku allurar shan inna – Inji Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

A jawabinsa, Shehin Malamin ya bayyana cewa har yanzu ba’a kammala yaki da cutar shan inna a Najeriya ba, don haka akwai bukatar iyaye su bada goyon baya wajen kawo karshen cutar a Najeriya gaba daya.

Shehi yayi alkawarin bada duk gudunmuwar data kamata don ganin an kawar da cutar shan inna daga Najeriya, dama sauran cututtukan dake addaban kananan yara , don yayi kira ga yan Najeriya dasu kai rahoton barkewar duk wani cuta ga hukumar data dace don shawo kansa.

Game da sha’anin satin kulawa da mata masu juna biyu kuwa, Malamin ya nemi iyaye, mata masu juna biyu da masu kula dasu yi amfani da wannan damar wajen samar ma mata da kananan yara ingantaccen lafiya.

Daga karshe Malamin ya jinjina ma gwamnati, abokan huldarta da kuma masu ruwa da tsaki bisa kokarin da suke yi na samar da ingantaccen kiwon lafiya a Najeriya.

Majiyarmu ta ruwaito dubun dubatan jama’a mabiya darikar Tijjaniyyah ne suka halarci taron rufe tafsirin na bana, wanda hakan ya kawo karshen karatun da Shehi keyi a kowacce Ramadan, sai kuma shekara mai zuwa idan Allah Ya kaimu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel