Sanata Bala kaura ya yi nade naden farko a matsayin gwamnan Bauchi

Sanata Bala kaura ya yi nade naden farko a matsayin gwamnan Bauchi

Sabon gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Kauran Bauchi yayi sabbin nade nade na farko a gwamnatinsa, inda ya nada Muhammad Baba a matsayin sakataren gwamnatin jahar Bauchi, da kuma Dakta Abubakar Kari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin gwamnan, Dakta Ladan Salihu ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu a garin Bauchi, inda yace nadin wadannan manyan jami’an gwamnatin ya fara nan take ne.

KU KARANTA: Sabon gwamna ya kara mata ta 3 kwana daya bayan darewarsa madafan iko

Sanata Bala kaura ya yi nade naden farko a matsayin gwamnan Bauchi
Sanata Bala kaura ya yi nade naden farko a matsayin gwamnan Bauchi
Asali: Facebook

Sauran mukaman da Gwamna Bala ya nada sun hada da Alhaji Bashir Yau a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da zai yi aiki a ofishin mataimakin gwamna Alhaji Baba Tela.

Haka zalika gwamnan ya nada mataimakin shugaban kungiyar yan jaridun Najeriya ta kasa, NUJ, Mukhtar Gidado a matsayin babban mashawarcinsa akan kafafen watsa labaru, Alhaji Umaruji Hassan a matsayin jami’in tsare tsare.

A ranar Laraba, 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da Bala Muhammed a matsayin sabon angon jahar Bauchi bayan ya samu nasara a zaben gwamnan jahar inda ya kayar da tsohon gwamna Muhammad Abubkar.

A wani labarin kuma bayan kwana daya tal da darewarsa kujerar gwamna, sabon gwamnan jahar Yobe Mai Mala Buni ya kara aure, inda ya auri diyar tsohon gwamnan jahar Yobe, Ibrahim Gaidam daya mika masa mulki a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.

Sunan amaryar Ummi Adama Gaidam, kuma a yanzu haka tana karatun digiri a wata jami’a dake kasar Saudi Arabia, sai Ummi zata shiga gidan sabon gwamnan ne a matsayin mace ta uku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng