Farawa da iyawa: Wani sabon gwamna yace ba zai iya biyan albashin N30,000 ba

Farawa da iyawa: Wani sabon gwamna yace ba zai iya biyan albashin N30,000 ba

Wasa farin girki, kamar yadda masu iya magana suke cewa, anan sabon gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde ne ya bayyana ma ma’aikatan jahar cewa shifa ba zai basu tabbacin biyan sabon karancin albashi na naira dubu talatin ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Makinde ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi bayan rantsar dashi a matsayin gwamnan jahar Oyo, gwamnan yayi alkawarin kara kaimi wajen karbar haraji da kuma rage kudin da ake kashewa wajen hidimar gwamnati.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ‘Sarkin garin Kano’ bai halarci taron rantsar da Ganduje karo na 2 ba

“A kwana kwanan nan ne gwamnatin tarayya ta sanar da sabon karin albashi, inda karamin ma’aikacin gwamnati zai samu naira dubu talatin a matsayin albashinsa, ina sane da amfanin da wannan kudi zai yi ma ma’aikata.

“Amma duba da halin da asusun jahar Oyo yake a yanzu, zan yaudareku ne kawai idan nace zan iya biyan wannan karancin albashi, nafi ganin kamata yayi a kyale jahohi su yanke ma kawunansu nawa zasu iya biya a matsayin karancin albashi duba da halin da suke ciki.

“Duka jahohin Najeriya ba daya suke ba, don haka bai dace a hadasu gaba daya ayi musu kudin goro ba.” Inji shi.

Sai dai daga karshe gwamnan ya bayyana manufarsa ta ganin cewa jahar Oyo ta biya karancin albashin daya haura N30,000, amma yace akwai bukatar hakuri da juriya saboda cigaba yana daukan lokaci kafin ya tabbata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng