An rantsar da gwamnan Kebbi a karo na biyu

An rantsar da gwamnan Kebbi a karo na biyu

A yau Laraba, 29 ga watan Mayun 2019, aka sake rantsar da gwamna jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu na jam'iyyar APC tare da mataimakin sa, Alhaji Samaila Yombe, a wani sabon wa'adin gwamnati na biyu.

Gwamna Bagudu tare da mataimakin sa sun karbi rantsuwa ne a babban ofishin Alkalin shari'a na jihar Kebbi, Mukhtar Jega, a safiyar yau cikin Birnin Kebbi inda suka sha alwashin gudanar da mulkin bisa gaskiya da adalci.

Gwamna Bagudu yayin karbar rantsuwa

Gwamna Bagudu yayin karbar rantsuwa
Source: Twitter

Bagudu cikin jawaban sa na karbar rantsuwa da shan alwashi ya bayar da tabbacin sa ga al'ummar Kebbi cewa nan ba da jimawa ba jihar za ta hau sahun jihohi masu samar da man fetur a kasar nan.

Ya ce gwamnatin sa cikin tsawon shekaru hudu da ta shafe a kan gado na mulki ta samu nasarorin gaske a fannin inganta kiwon lafiya, habaka harkokin ilimi, samar da wutar lantarki, ci gaba gine-gine da kuma harkokin noma.

KARANTA KUMA: Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana kadarar sa

Kazalika gwamna Bagudu ya kwarara godiya ga al'ummar jihar Kebbi da suka yaba da kwazon gwamnatin ta da a halin yanzu suka sake ba shi wata dama ta rataya masa nauyin riko da akalar jagoranci a karo na biyu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel