Mata zasu fara limancin sallah a Ghana

Mata zasu fara limancin sallah a Ghana

- Wata mata a kasar Ghana ta na kokarin fito da wani sabon lamari na addinin Musulunci

- Matar ta fara yunkurin nemawa mata 'yancin jagorantar sallah a masallatai

- Yanzu haka dai matar tana nan ta dage da gabatar da wa'azi ga mata mabiyanta

Wani fitaccen malami Imam Mustapha Abdullah shine yake jagorantar sallar kamsus salawati a masallacin Kpalsi da ke birnin Tamale a yankin arewacin Ghana. Malamin ya saba raba sahu tsakanin maza da mata da suke zuwa masallacin nashi salla ta hanyar amfani da labule a tsakaninsu, saboda addinin musulunci bai yarda maza da mata su cakudu a wuri daya ba, sannan kuma addini bai halattawa mata su yi limanci ba.

Sai dai kuma Hajiya Hawlatu Abdallah tana son ta mayar da wannan tsari na addini ya zama tarihi. Hasali ma a cikin wannan wata na Ramadana, wata masu yawan gaske suna halartar wa'azin da take yi. Hajiya Hawlatu ta ce tana da yakinin abinda take yi yana da matukar tasiri ga mata.

Mata zasu fara limancin sallah a Ghana

Mata zasu fara limancin sallah a Ghana
Source: Facebook

A hankalia a hankali mata sun fara amfani da koyarwar ta, in ji wata mata mai suna Ayishetu Adams, wacce take daya daga cikin matan da suke halartar wa'azin Hajiya Hawlatu.

Sai dai kuma Imamu Mustapha ya bayyana cewa akwai iya hurumin da mace ya kamata tayi wa'azi a kai a Musulunci.

KU KARANTA: Kasashe 50 da suka fi yawan al'umma a duniya

An sha ganin mata na tilawar karatun Alkur'ani a kasar Ghana. Amma kuma suna fuskantar matsala a fannin jan sallah a masallatai. Hakan ne yasa wasu mata kamar irin su Hamida Alhassan suke ganin cewa lokaci yayi da ya kamata a samu canji. Inda ta ke cewa, "Akwai 'yar uwata da ta sauke Alkur'ani, saboda haka banga abinda zai sa mace baza ta iya jagorantar mutane sallah ba. Ina ganin cewa mace na iya jagorantar mutane saboda na ga wata mata tana jagorantaar sallah. Saboda haka ina ganin kamar lokaci yayi da za a bai wa mata wannan dama ta jagorantar sallah."

Matan da suke da wannan akidar basu taka kara ya karya ba a kasar Ghana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Online view pixel