Kai tsaye: Bikin rantsar da shugaban kasa da mataimakinsa
An rufe taron rantsar da Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo. Sai dai shugaban bai yi jawabi ba, kamar yadda ya yi a shekarar 2015 lokacin da ya dauki rantsuwar fara mulkin wa'adinsa na farko.
An karanto tarihin Shugaba Buhari yayin da shi kuma yake ci gaba da kewaye dandalin Eagle Square a cikin wata mota yana jinjina ga jama'a.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu a yau Laraba, 29 ga watan Mayu.
Shugaban alkalan Najeriya, Justis Mohammed Tanko ne ya rantsar da shugabannin biyu.

Asali: Twitter
A yanzu haka, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Oinbajo ya dauki rantswar kama aiki a karo na biyu.

Asali: UGC
Farfesa Shehu Galadanci ne zai bude taron rantsa da shugabannin da addu'ar addinin Musulunci.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda za a rantsar da shi tare da Mataimakinsa Yemi Osinbajo a wa'adin mulki na biyu.
Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ma ya isa dakin taro na Eagle Sqare.
Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Yakubu Gowon da tsohon Shugaban kasa, Cif Ernest Shonekan na daga cikin manyan mutanen da suka isa filin taro na Eagle Square a Abuja, wajen bikin rantsar da Shugaban kasa a yau Laraba, 29 ga watan Mayu.
Za a rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo a wajen taron.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa har yanzu tsoffin Shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Ibrahim Badamasi Babangida basu hallara ba a wajen taron.
Sauran manyan mutanen da suka hallara sun hada da mambomin kungiyar sojojin diflomasiyya, manyan yan kasuwa, Aliko Dangote, gwamnoni, jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yan majalisa da sauransu.
An tattaro cewa an tsaurara matakan tsaro a wajen taron.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta samar da ayyuka miliyan 20 a zangon Buhari na 2 - Minista
A baya Legit.ng ta rahoto cewa ma’aikatan FRSC akalla 2000 za a jibge a cikin babban birnin tarayya Abuja a dalilin bikin rantsuwar da ake yi yau Laraba 29 ga Watan Mayu.
Wani babban jami’in hukumar FRSC masu kula da tituna a Najeriya, Mista Gora Wobin, ya bayyana cewa za a baza ma’aikata da za su lura hanyoyi a yayin da ake sake rantsar da shugabannin Najeriya.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng