Taba kidi taba karatu: Jerin hutun da 'yan Najeriya za su samu a cikin wannan shekarar
- Karshen shekarar 2019 zai zamo abin farin ciki ga 'yan Najeriya saboda hutun da za su samu ciki har da wanda za a yi yau dinnan
- Majiyarmu Legit.ng ta yi kokarin kawo muku jerin hutun da 'yan Najeriya za su samu a cikin wannan shekarar
Kwanan nan gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta mayar da ranar 12 ga watan Yuni ya zama ranar dimokuradiyya na Najeriya, domin tunawa da ranar 12 ga watan Yuni, 1993, da Cif MKO Abiola ya lashe zabe.
Za a cigaba da amfani da tsohuwar ranar dimokuradiyya ta 29 ga watan Mayu don tunawa da farkon shekaru hudu na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Duka kwanaki biyun an bayyana su a matsayin ranekun hutu ga 'yan Najeriya.
A lokacin da yake sanarwar, Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce, "An aika da gayyata zuwa ga shugabannin duniya don su samu halartar bukukuwan da za ayi din."
Ya kara da cewa bikin da za ayi yau, ba zai ayi wata hidima da yawa ba, saboda kasar nan ba za ta iya kashe kudi wurin gabatar da bukukuwa guda biyu a cikin sati biyu ba.
Majiyarmu ta yi kokarin kawo muku jerin hutun da 'yan Najeriya zasu samu a wannan shekarar:
Ranar rantsar da shugaban kasa (Mayu 29)
Najeriya ta fara bikin ranar 29 ga watan Mayu a matsayin ranar dimokuradiyya a shekarar 2000. Sai dai kuma an samu canjin hakan a watan Yunin shekarar 2018, bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canja ranar daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Mayu.
Hutun karamar sallah (Yuni 5)
Ana bikin karamar sallah a karshen kowanne watan Ramadana, wanda musulmai suke yin azumi na tsawon kwanaki 30 . Ranar na canjawa a kowacce shekara, ya danganta da ranar da aka ga sabon wata. A wannan shekarar dai ana sa ran za ayi bikin karamar sallar ranar5 ga watan Yuni.
Ranar dimokuradiyya (Yuni 12)
An mayar da ranar dimokuradiyya 12 ga watan Yuni. Saboda tunawa da ranar 12 ga watan Yuni, 1993, da Cif MKO Abiola ya lashe zabe a kasar nan.
Hutun babbar sallah (Agusta 12)
Wannan shine babban biki a gurin al'ummar musulmai. Ana samun bambancin ranar a kowacce shekara, ya danganta da ranar da aka ga wata. A wannan karon dai ana sa ran za ayi bikin ranar Litinin 12 ga watan Agusta.
KU KARANTA: An samu nasarar kubutar da matar dan majalisa da 'ya'yansa guda biyu da aka sace a jihar Gombe
Ranar samun 'yancin kai (Oktoba 1)
Ana yin wannan hutu ne a Najeriya don tunawa da samun 'yan cin kan Najeriya daga Birtaniya. Wannan karon hutun zai zo ranar Talata ne.
Ranar Kirsimeti (Disamba 25)
Ranar Kirsimeti ita ce ranar murnar haihuwar Yesu Almasihu. Ranar hutu ce a mafi yawancin kasashe ciki kuwa hadda Najeriya. Wannan karon za ayi hutun ranar Laraba ne.
Ranar Dambe (Disamba 26)
Ana gabatar da wannan hutun ne kwana daya bayan an yi hutun Kirsimeti. Shi kuma za ayi shi ranar Alhamis ne.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana
Asali: Legit.ng