Sakkwatawa sun kaurace wa wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto (Hotuna)

Sakkwatawa sun kaurace wa wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto (Hotuna)

A yayin da aka gudanar da bukukuwan rantsar da sabbin gwamnoni da aka zaba a karo na farko da na biyu da kuma shugaban kasa da mataimakinsa, bikin rantsar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwa, bai samu halartar jama'ar Sokoto ba kamar yadda aka gani a wasu jihohi.

Rahotanni sun bayyana cewar duk wanda ya shiga cikin babban birnin Sakkwato zai ga jama'a na gudanar da al'amuransu kamar yadda suka saba, wasu ma tamkar basu san cewa yaune ake bikin rantsar da zababbun shugabanni ba.

Mustapha Dingyadi na da ra'ayin cewa halartar rantsuwar bata da wani tasiri domin kuwa nan da dan lokaci kadan kotu zata karbe kujerar gwamnan ta bawa dan takarar jam'iyyar APC.

Sakkwatawa sun kaurace wa wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto (Hotuna)

Sakkwatawa sun kaurace wa wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto
Source: Facebook

Sakkwatawa sun kaurace wa wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto (Hotuna)

Wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto
Source: Facebook

Sakkwatawa sun kaurace wa wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto (Hotuna)

Wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto
Source: Facebook

A babban filin kangiwa square, filin taron bikin rantsar da Tambuwal, bikin rantsuwar bai samu tagomashi ba daga wurin Sakkwatawa ba, domin kuwa sun qauracewaba wurin, lamarin da aka bayyana a baya ba haka rantsuwa ke gudana a jihar ba.

DUBA WANNAN: Tsofin gwamoni 4 a mulkin soji sun halarci bikin rantsar da Badaru a jihar Jigawa

"Na tabbata da gwamna Tambuwal nada masaniyar zaayi irin wannan abin kunyar toh da sai ayi wannan bukin a ofishinsa dake Gidan gwamnati

"An shafe kusan wata da watanni ana sanarwar gayyatar wannan bukin amman kasancewar Sakkwatawa ALU sukeyi ba jam'iyaba sun ki amsa kiran Tambuwal," a cewar Dingyadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel