Yan bindiga sun hallaka mutu 23 a kauyukan Zamfara 2

Yan bindiga sun hallaka mutu 23 a kauyukan Zamfara 2

Yan bindiga a ranar Talata, 28 ga watan Mayu sun kashe akalla mutane 23 a hare-haren da suka kai kauyukan Tunga da Kabaje, yankin Sakajiki dake karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.

Al’umman yankin sun ce yan bindigan sun shigo da yawansu da misalin karfe 5:30 na safe bayan suhur inda suka soma harbe harbe.

Sun ce an far ma wasu daga cikin mutanen da lamarin ya cika dasu sannan aka kashe su a gonaki.

“Abunda ya faru shine yan banga wadanda aka fi sani da ‘yan sakai’ sun kashe wani dan acaba maidake goye da matar wani dan bindiga da dansa daga jejin dake kusa da kauyen, ana zargi dan acaban da kai ma yan bindiga rahoto a jejin.

Yan bindiga sun hallaka mutu 23 a kauyukan Zamfara 2

Yan bindiga sun hallaka mutu 23 a kauyukan Zamfara 2
Source: Depositphotos

“A haka ne, aka dunga sa mishi ido inda aka gano shi goye da mata da yaron daya daga cikin wanda ake zargin dan bindiga ne.

“Musabbabin haka ne aka kashe dan acaban tare da fasinjojinsa. Muna zatton wannan ne sanadiyyar ramuwa da yan bindigan suka daukaka. A halin yanzu da nake muku magana, muna a makabarta don binne wadanda suka rasa rayukansu.”

KU KARANTA KUMA: Anyi garkuwa da mutane 2 yayinda yan bindiga suka kai hari kauyen Dan Ali

Wani mazaunin kauyen Aliyu Yushau yace, “ga jiragen sojin sama suna shawagi a sama don neman sansanin yan bindigan. Muna tare da sojojin da sauran jami’an tsaro”.

A halin yanzu, shugaban karamar hukumar Kaura Namoda Alhaji Lawal Isah Abdullahi ya tabbar da harin inda yace ana kokarin ganin an binne wadanda suka mutu tare da bada kariya ga sauran kauyukan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel