Aisha Buhari ta yi bude baki tare da Zainab Aliyu da ahlin gidansu a fadar shugaban kasa (hotuna)

Aisha Buhari ta yi bude baki tare da Zainab Aliyu da ahlin gidansu a fadar shugaban kasa (hotuna)

- Zainab Aliyu wacce aka kama kan laifin safarar miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya ta ziyarci fadar Shugaban kasa

- Matashiyar mai shekaru 22 ta ziyarci Uwargidar Shugaban kasa tare da ahlin gidansu

- An gano su suna liyafar bude baki tare da uwargidar Shugaban kasar

Matashiyar nan mai suna Zainab Aliyu ta ziyarci fadar Shugaban kasa a Abuja tare da ahlin gidansu. Matashiyar da ahlin gidan nasu sun amsa gayyatar uwargidar Shugaban kasa, Aisha Buhari ne.

Legit.ng ta rahoto a baya cewa Zainab Aliyu, wacce akka zarga da safarar miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya bisa kuskure, tayi Magana. Yarinyar mai shekaru 22 a duniya ta shafe watanni 4 a gidan kurkukun kasar Saudiyya.

Aisha Buhari ta yi bude baki da Zainab Aliyu da ahlin gidansu a fadar Shugaban kasa (hotuna)

Aisha Buhari ta yi bude baki da Zainab Aliyu da ahlin gidansu a fadar Shugaban kasa
Source: Twitter

Tayi ikirarin cewa a zaman da tayi a gidan yari ya bata daman koyon tsantsar larabci da kuma haddar rabin Al-Qur’ani.

Aisha Buhari ta yi bude baki da Zainab Aliyu da ahlin gidansu a fadar Shugaban kasa (hotuna)

Aisha Buhari ta yi bude baki da Zainab Aliyu
Source: Twitter

A sabbin hotunan da Abike Dabiri-Erewa ta wallafa a shafin twitter, an gano matashiyar mai shekaru 22 a fadar Shugaban kasa tare da ahlin gidansu da kuma uwargidar Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari.

Aisha Buhari ta yi bude baki da Zainab Aliyu da ahlin gidansu a fadar Shugaban kasa (hotuna)

Aisha Buhari ta yi bude baki da Zainab Aliyu da ahlin gidansu
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: 29 ga Mayu: Kano ta kaddamar da yau Talata a matsayin ranar addu’a a fadin kananan hukumomi 44

A cewar Dabiri-Erewa, iyalan sun yu bude baki (Iftar) tare da uwargidar Shugaban kasa. Ta kuma bayyana cewa ya zama dole bangaren shari’a ta tabbatar da hukunta wadanda suka yiwa Zainab bakin fenti.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel