Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu

Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara mulkinsa karo na biyu a ranar Alhamis 29 ga watan Mayu bayan an rantsar da shi sakamakon lashe zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2019.

Duk da nasarar da ya samu a zaben na Fabrairun 2019, mulkinsa na shekaru hudu masu zuwa ba za su kasance ba tare da kallubale ba kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.

A cewar Bloomberg, akwai wasu muhimman abubuwa 10 da ke bukatar shugaban kasa ya mayar da hankali a kansu cikin gaggawa:

Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu

Next Level: Muhimman abubuwa 8 da kamata Buhari ya mayar da hankali a kansu
Source: Twitter

1. Darajar Naira

Masu saka hannun jari musamman na kasashen waje sun rika nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin Najeriya ke sarrafa Naira a cikin shekaru hudu da suka shude musamman bayan faduwar farashin kudin mai.

2. Farashin man fetur

Farashin kudin man fetur a Najeriya shine na shida cikin jerin kasashen da man fetur yafi araha inda ake sayar da litan mai kan N145. A shekarar 2018, gwamnati ta kashe Dalla Biliyan 2 wurin biyan tallafin man fetur kuma Bankin Bayar da Lamuni na duniya IMF ta shawarci gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur domin magance matsalar.

3. Rashin Wutan Lantarki

Najeriya ta dade tana fama da rashin ingantaccen wutan lantarki kuma matsalar da gaggari gwamnatocci da dama magancewa.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi alhinin mutuwar Dr Ibrahim Lame

4. Cikinso a tashoshin sauke kaya

Baya ga matsalar rashin wutar lantarki, wani babban matsala da ke adabar Najeriya shine cinkoso da ake samu a tashoshin sauke kaya hakan yasa shugaban kasa ya bayar da umurnin ayi gaggawar kawar da kayyakin.

5. Boko Haram

Wani muhimmin fanni da ke bukatar shugaban kasa ya dauki mataki a kai shine kallubalen 'yan ta'adan Boko Haram da ke adabar mutanen yankin Arewa maso Gabas.

6. Yaki da Rashawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi suna wurin yaki da rashawa musamman tsakanin magoya bayansa. Sai dai masu adawa da shi suna kokawa da irin sallon yaki da rashawarsa.

7. Hannun jarin kasashen waje

Bloomberg ta ruwaito cewa masu saka hannun jari daga kasashen waje sun ragu a karkashin gwamnatin Buhari duba da rikicin da gwamnatinsa tayi da kamfanoni kamar MTN da JP Morgan Chase & Co. A 2018 Najeriya da samu $2.2bn daga masu hannun jarin kasashen waje wanda hakan bai kai kashi daya cikin uku na abinda kashen Afrika ta Kudu da Egypt suka samu ba.

8 . Hayayafar al'umma

Yawan al'ummar da ke Najeriya sun kai Miliyan 201 a 2018 kuma hasashen Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa ana sa ran za su kai Miliyan 410 a shekarar 2050 wanda hakan na nuna Najeriya za ta fi kasashe kamar India da China yawan mutane.

Masu saka hannun jari suna da mabanbantan ra'ayoyi a kan lamarin, wasu na ganin abu mai kyau ne yayin da wasu ke ganin hakan zai haifar da yawan aikata laifuka tsakanin mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel