Zababben gwamnan Adamawa ya sha alwashin bincikar Bindow, yace a shirye yake ya taka kowa

Zababben gwamnan Adamawa ya sha alwashin bincikar Bindow, yace a shirye yake ya taka kowa

Ahmadu Fintiri, zababben Gwamnan jihar Adamawa, yace a shirye yake don tabbatar da magance rashin adalcin da gwamnatin Gwamna Jibrilla Bindow mai barin gado ya aiwatar akan al’umman jihar.

Mista Fintiri ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Yola yayinda yake karban rahoto daga mambobin kwamitin mika mulki 67.

Yace binciken kwamitin ya nuna an keta tsari da kuma rashin kashe kudaden gwamnati a wajen gudanar da ayyuka wanda ya kamata ayi bincike a kai.

Zababben gwamnan Adamawa ya sha alwashin bincikar Bindow, yace a shirye yake ya taka kowa
Zababben gwamnan Adamawa ya sha alwashin bincikar Bindow, yace a shirye yake ya taka kowa
Asali: UGC

Yayinda yake korafin cewa gwamnati mai barin gado ta karbi kimanin naira biliyan 332 daga gwamnatin tarayya ba tare da an gudanar da ayyuka ba, Mista Fintiri yace gwamnatinsa zata gudanar da bincike mai zurfi akan rahoton tare da aiwatar da muhimman shawarwari.

Yayin da yake gabatar da rahoto a baya, shugaban kwamitin, Aliyu Ismaila, yace gwamnati mai barin gado tayi almubazaranci a fannoni da dama na jihar tare da barin bashi har na biliyan 115.

KU KARANTA KUMA: Canje-canje da majalisa tayi zasu shafi aiwatar da kasafin kudin 2019 - Buhari

“Abun bakin ciki ne ganin cewa gwamnati mai barin gado tun daga asali, ta kasance tana daukan bashi ne don biyan albashin yayin da ba ayi amfani da kudaden shiga wajen gudanar da ayyukan da zai amfani masu biyan haraji ba a jihar."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng