Abubuwan da Buhari zai aikata a zangon mulkinsa na karshe – Fadar shugaban kasa

Abubuwan da Buhari zai aikata a zangon mulkinsa na karshe – Fadar shugaban kasa

Yayin daya rage saura kwanaki biyu a rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya karo na biyu a ranar Laraba 29 ga watan Mayu, fadar shugaban kasa tayi karin haske game da wasu ayyuka masu muhimmanci da Buhari zai karkatar da hankalinsa garesu.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da yayi da jaridar Weekly Trust, inda yace yan Najeriya zasu ga sabon shugaba Buhari mai kwazo da kuzari.

KU KARANTA: Buhari ya nada Farfesa Hamidu a matsayin shugaban asbitin koyarwa na ABU dake shika

Abubuwan da Buhari zai aikata a zangon mulkinsa na karshe – Fadar shugaban kasa

Buhari shugaban kasa
Source: Twitter

Malam Garba yace shugaba Buhari zai kara azama da kaimi wajen aiwatar da dukkanin alkawurran daya daukan ma yan Najeriya, tare da daurawa akan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a wa’adin mulkinsa na farko.

Wasu daga cikin manyan ayyukan da Garba Shehu ya zayyana sun hada da:

- Inganta harkar sufurin jirgin kasa dana jirgin sama

- Kammala shimfida titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan

- Farawa tare da kammala shimfida titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano

- Inganta harkar samar da wutar lantarki

- Gyara a sha’anin kiwon lafiya

- Shawo kan rikicin makiyaya da manoma

- Kawon karshen hare haren yan bindiga da satar shanu

Kaakakin ya kara da cewa ya zama dole a jinjin ma shugaba Buhari bisa rawar ganin daya taka wajen gurgunta ayyukan Boko Haram, inda yace da zuwa Buhari Boko Haram na rike da kananan hukumomi 21, amma a yanzu dakarun Sojin Najeriya dana kasashe makwabta sun ci karfinsu.

Daga karshe ya kara da cewa gwamnatin Buhari zata cigaba da baiwa hukumomin tsaron Najeriya gudunmuwar data kamata domin gamawa da Boko Haram gaba daya da kuma sauran ayyukan yan bindiga da suke damun Arewacin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel