Karin haske a kan abin da ya hana Buhari ganawa da Sarkin Saudi a lokacin da ya je Umrah

Karin haske a kan abin da ya hana Buhari ganawa da Sarkin Saudi a lokacin da ya je Umrah

A kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je kasar Saudiyya har yayi ibadar Umrah. Mun fahimci cewa wannan ziyara ta shugaban kasar Najeriyar ta jawo abin magana a gida.

Idan ba ku manta ba, fadar shugaban kasar tayi ikirarin cewa Sarkin Saudiyya Salman Bn Abdulaziz ne ya gayyace sa zuwa kasar mai tsarkin domin yayi ibada a cikin lokacin azumin Ramadan.

Sai dai har shugaban kasar ya je ya dawo bai hadu da Sarkin kasar Saudiyyan kamar yadda aka sanar ba. Daga bayan Hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ya fayyace abin da ya jawo hakan.

Mista Bashir Ahmaad, wanda yana cikin masu taimakawa shugaban kasar a kafafen sadarwa na zamani ya bayyana cewa shugabannin Saudiyya ba su ganawa da baƙi a lokacin da ake Watan azumi.

KU KARANTA: Yadda za ayi maganin mugum kishin ruwa a lokacin azumi

Karin haske a kan abin da ya hana Buhari ganawa da Sarkin Saudi a lokacin da ya je Umrah

Shugaba Buhari da wasu manya a wajen aikin Umrah
Source: Facebook

Hadimin shugaban kasar yake cewa idan gwamnatin Saudi ta gayyaci mutum zuwa Umrah, bai nufin cewa zai gana da Sarakunanta, sai dai hakan na nufin an shirya masa tanadi na musammana kasar.

Bashir Ahmaad yake cewa:

“Ya kamata wasu su san cewa goron gayyatar Umrah daga kasar Saudi bai nufin cewa za a zauna da Sarkin Saudiyyar ko wani jami’in gwamnatin kasa mai tsarkin.

“Saudiyya ba ta bari shugabannin Duniya su yi Umrah a lokacin da ake azumi a dalilin irin cinkuson da ake yi a kasar…”

Mista Ahmad ya kare da cewa:

“…Goron gayattar Saudi yana nufin cewa an shiryawa shugabannin kasashen tanadi na musamman da za su yi ibada tare da tawagarsu ba tare da an matsawa sauran masu ibada ba…”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel