2019: Ina so ne in zama Abokin hamayyar Gbajabiamilla inji Bago

2019: Ina so ne in zama Abokin hamayyar Gbajabiamilla inji Bago

Mun ji cewa Umar Bago wanda zai koma majalisar tarayya a karo na uku wannan karo, ya fito ya bayyana cewa takarar kujerar majalisar wakilai da yake yi a bana, ba fito-na-fito bane da jam’iyyar APC.

Honarabul Umar Bago mai wakiltar yankin Chanchanga a majalisar tarayya yake cewa bai da niyyar batawa jam’iyyarsa ta APC mai mulki rai da takarar da yake wajen neman kakakin majalisa.

Bago yake cewa ya tsaya takara ne domin samawa wanda ‘dan takarar da APC ta tsaida Abokin hamayya. Honarabul Bago yake cewa sam bai fito takara da nufin sabawa matakin jam’iyya ba.

Shugaban kwamitin na harkar ruwa a majalisar wakilan tarayya ya bayyana wannan ne a lokacin da ya halarci wani taron laccar Watan azumi da aka shirya a cikin Garin Iseyin da ke cikin jihar Oyo.

KU KARANTA: Ana so Kotu ta hana Gbajabiamilla takarar kujerar Majalisa

Wani ‘dan majalisa kuma Abokin aikin Umar Bago da ke yankin watau Honarabul Shina Peller. Mai wakiltar mazabobin Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa ne ya shirya wannan taro ya gayyaci Umar Bago.

Umar Bago ya fadawa Manema labarai cewa ya ba ‘yan majalisa dama su zabi duk wanda su ke so a gwabzawar da za ayi kwanan nan. Bago yake tunawa jama’a cewa majalisa tana cin gashin kan-ta ne.

‘Dan majalisar na APC yake cewa duk da haka majalisa za tayi aiki hannu-da-hannu da masu rike da madafon iko ta hanyar kawo dokoki da za su taimakawa tsare-tsaren gwamnatin Najeriya idan ya dace.

Wadanda su ka halarci wannan taro na Watan azumi da aka shirya sun hada da ;yan majalisar tarayya fiye da 40 daga jihohin Oyo, Legas, Borno, Yobe da wasu manyan APC da dai sauran su

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel