Tsohon shugaban kwallon kafa na kasa, ya shiga layin 'yan takarar gwamnan jihar Kogi

Tsohon shugaban kwallon kafa na kasa, ya shiga layin 'yan takarar gwamnan jihar Kogi

- Tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa na Najeriya, Sani Lulu ya fito takarar gwamnan jihar Kogi a karo na farko

- Tsohon shugaban ya fito takarar ne karkashin inuwar jam'iyyar APC, inda yayi wa mutanen jihar gabatar da sahihin mulki idan suka zabe shi

Tsohon shugaban 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya, Sani Lulu, shima ya bi sahun 'yan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress APC mai mulki.

Lulu wanda ya bayyana manufar shi ga al'umma a lokacin da yake wata hira a Abuja, ya ce akwai abubuwa da dama da suke nuna cewa gwamnatin da ake ciki ta yanzu, ta kasa cika alkawuran da ta dauka lokacin yakin neman zabe. Hakanne ya sanya dole ya fito domin ceto jihar daga halin da take ciki.

Tsohon shugaban kwallon kafa na kasa, ya shiga layin 'yan takarar gwamnan jihar Kogi
Tsohon shugaban kwallon kafa na kasa, ya shiga layin 'yan takarar gwamnan jihar Kogi
Asali: UGC

Ya ce zai yi amfani da kwarewar da yake da ita a lokacin da ya jagoranci 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya, inda sanadiyyar shi ne yasa suka dinga samun nasara a wancan lokacin.

"Shiga wannan sabuwar gwamnatin na nufin kowanne dan Najeriya ya fito a dama dashi, amma mu a jihar Kogi zamu yi na mu daban dana kowa. Na gama yanke hukunci akan kuduri na, kuma ina fatan da hadin kanku zamu kai jihar gaci.

"Dukkan mu nan mun san cewa wannan gwamnati da muke ciki ta kasa yin komai a jihar nan, saboda haka idan wani zai zo, dole ne yayi nashi aikin daban da na yanzu," in ji shi.

KU KARANTA: Kotu ta bada oda a kamo tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu

Lulu ya ce idan har aka bashi dama zai tabbatar da cewar gwamnatinsa ta zama mai gaskiya da rikon amana, kuma zai tabbatar da cewar ya rufe duk wata baraka, saboda al'ummar jihar su san cewa sun samu canjin gwamnati.

"Jam'iyyar APC ta na kokarin kawo gyara a kasar nan. Dukkan mu da muke kokarin fitowa takara mun ga ya kamaata mu fito ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar misali akan kowa, kuma muma abinda muke so muyi kenan, muna so muyi koyi dashi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel