Wata kotu ta sake hana Ganduje kafa sabbin masarautu

Wata kotu ta sake hana Ganduje kafa sabbin masarautu

Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin Justis Ahmed Tijjani Badamasi ta hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kafa sabbin masarautu a jihar.

Justis Badamasi ya kuma umurci gwamnan da ya janye daga nada kowa a matsayin sarki a sabbin masarautun.

Alkalin ya kuma yi umurnin cewa ayi gaggawan aiwatar da odar ta hanyar wallafawa a jaridar Daily Trust.

Wannan ita ce kotu na biyu da ke bayar da irin wannan umurni na hana gwamnan kafa masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye.

Wata kotu ta sake hana Ganduje kafa sabbin masarautu

Wata kotu ta sake hana Ganduje kafa sabbin masarautu
Source: UGC

Da farko dai wata babbar kotu a jihar, karkashin jagorancin Justis Nasiru Saminu ta mayar da umurni makamancin haka.

Justis Badamasi ya bayar da umurnin a jiya Alhamis, 23 ga watan Mayu bayan wata kara da masu nada sarki a Kano su hudu, Sarkin Bai Alhaji Mukhtar Adnan, Makaman Kano Alhaji Sarki Ibrahim Makama, Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani da kuma Sarkin Dawaki Maituta Alhaji Bello Abubakar suka shigar.

Masu karar na kalubalantar kafa sabbin masarautu hudu ne a jihar.

KU KARANTA KUMA: Kano: Ma'aikata sun shiga dar-dar yayin da Ganduje ya ciyo bashin dala miliyan 95

Sauran bangarorin da aka shigar a karar sun hada da kakakin majalisar dokokin jihar Kano Kabiru Alhassan Rurum; Atoni-janar na jihar, Sarkin Gaya Ibrahim Abdulkadir Gaya; Sarkin Rano Tafida Abubakar Ila, Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar ll da kuma Alhaji Aminu Ado Bayero.

Justis Badamasi ya dage shari’an zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin fara sauraron karan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel