Za’a koma gidan jiya: Malaman jami’a zasu koma yajin aikin ‘sai baba ta ji’
Kungiyar Malaman jami’a ta ASUU ta dauki alwashin sake komawa yajin aiki matukar gwamnati bata cika alkawarin data daukan mata ba, musamman a yanzu da tace ta fahimci gwamnati na sanyi sanyi wajen zartar da yarjejeniyar da suka kulla a baya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyar tana cewa dama fa ba wai ta janye yajin aikin na dindindin bane haknan, sai data shimfida sharadin cewa janyewar wucin gadi tayi, kamar yadda shugabanta, Biodun Ogunyemi ya bayyana.
KU KARANTA: Matsalar tsaro: Tawagar manyan hafsoshin Soja da Yansanda sun sauka jahar Katsina
Shugaban na ASUU yayi wannan barazana ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu, inda yace har yanzu gwamnati bata nuna wasu alamun zartar da yarjejeniyar data shiga da kungiyar a shekarar 2019 ba.
Duk da cewa Ministan Ilimi Adamu Adamu yace gwamnati ta antaya ma ASUU naira biliyan 25, amma shugaban ASUU yace bashi da masaniya game da wannan kudi, kuma yace babu wani malamin jami’a daya samu wadannan kudade.
“Kamata yayi ace gwamnati ta biya wannan kudi tun a watan Feburairun shekarar 2019 a matsayin wani kaso na bashin alawus alawus da malaman jami’a suke binta, amma sai yanzu take cewa wai ta biya, kuma babu wata jami’a data tabbatar da samun wannan kudi.
“Don haka zamu sake zama da yayan kungiyarmu don sanin matakin daya kamata mu dauka, yayan kungiyarmu sun son yin aikinsu yadda ya kamata, amma ba zamu jure yadda gwamnatike rikon sakainar kashi da alkawurran data daukan mana ba.” Inji shi.
Idan za’a tuna a watan Nuwambar shekarar data gabata ne ASUU ta shiga yajin aiki inda ta kwashe watanni uku don nuna bacin ranta game da halin ko in kula da tace gwamnati na nuna ma ilimi a matakin jami’a.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng