Jariri ya rasu a ciki saboda Mahaifiyarsa ta guji zuwa gaban Likita a Ebonyi

Jariri ya rasu a ciki saboda Mahaifiyarsa ta guji zuwa gaban Likita a Ebonyi

Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya na jihar Ebonyi, sun tabbatar da cewa wata Baiwar Allah mai dauke da juna-biyu ta kashe Yaron da ke cikin na ta a yayin da ta ke ta faman nakudar haihuwarsa.

Wannan abin takaici ya faru ne a makon nan a Garin Abakaliki na jihar Ebonyi. Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Punch, wannan abu ya faru ne a jiya Laraba 22 ga Watan Mayun 2019.

Kakakin ‘Yan Sandan jihar Ebonyi, DSP Loveth Odah, ta bayyanawa manema labarai cewa wannan mata mai kusan shekaru 40 a Duniya ta ji wa kan-ta ciwo ne a wajen haihuwar yaron.

KU KARANTA: An ba Maza shawarar irin Matan da za su aura

Odah take cewa Baiwar Allah tayi kokarin ta haifi yaron ne da karfi-da yaji, kuma ba tare da taimakon Malaman da ke karbar haihuwa ba wanda wannan ya jawo ta rasa yaron tun a cikin ta.

Yanzu haka wannan Matar tana babban asibitin koyon aikin nan na Alex Ekwueme da ke cikin Garin Abakaliki. Wannan mata ta guji zuwa ganin Likita ne har sai da ‘Yan Sanda su ka matsa mata.

An bada umarni cewa a cigaba da kula da lafiyar ta a asibitin har sai ta samu sauki. Bayan nan kuma za a dauke ta zuwa ofishin ‘Yan Sanda domin ayi bincike kan yadda wannan jaririn ya mutu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel