Gwamnan jihar Kwara ya rushe majalisarsa

Gwamnan jihar Kwara ya rushe majalisarsa

- Gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed ya dakatar da dukkanin 'yan majalisar fadarsa

- Dakatarwar nasu zai fara aiki ne daga yau Larabar nan 22 ga watan Mayu

- Hakan na zuwa ne yan kwanaki kadan kafin rantsar da sabbin gwamnonin jihohi a fadin kasar wanda za a yi a ranar 29 ga watan Mayu

Gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed ya dakatar da dukkanin 'yan majalisar fadarsa daga yau Larabar nan 22 ga watan Mayu 2019.

A cewar wata sanarwa da mataimakin sakataren yada labarai na jihar ya fitar a yau Laraba, Mista Demola Olanrewaju, ya bayyana mutanen da abin ya shafa, wadanda suka hada da masu bada shawara ta musamman, mataimaka na musamman da kuma manyan mambobi na ma'aikatun gwamnati.

Gwamnan jihar Kwara ya rushe majalisarsa

Gwamnan jihar Kwara ya rushe majalisarsa
Source: UGC

Sanarwar ta bayyana yadda gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed yake mika godiyarsa ga mutanen da abin ya shafa, wadanda suka hada da tsofaffin masu taimaka masa da kuma mutanen da aka basu mukamai na siyasa, ga irin jajircewar da suka yi wurin ganin gwamnatinsa ta yi aiki tukuru ga al'ummar jihar.

KU KARANTA KUMA: Tiriliyan 1.2 mu ka zuba a asusun Gwamnatin Najeriya bara – NNPC

Hakan kuma gwamnan ya yiwa tsofaffin kwamishinoni da wasu manya na gwamnatinsa fatan alkhairi a rayuwarsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel