Hanyoyi 8 na kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane

Hanyoyi 8 na kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane

Cikin kwanaki bakwai da suka gabata, daruruwan 'yan Najeriya a fadin kasar nan ka ma daga masu hannu da shuni da kuma sabanin haka, sun tsunduma cikin tarkon masu ta'addancin garkuwa da mutane a yayin da annobar ta zamto ruwan dare.

Ko shakka babu ta'addancin masu garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa ya ci gaba da ta'azzara a fadin kasar nan gami da kai wa matakin intaha wajen bayyana gazawar gwamnati karara ta fuskar rashin samar da ingataccen tsaro.

Hanyoyin kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane

Hanyoyin kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane
Source: Facebook

Domin kauce wa afkawa tarkon masu wannan mummunan ta'ada gami da zalunci tsagwaran sa, majiyar mu da sanadin jaridar The Nation ta kawo muku jerin wasu muhimman hanyoyi na riga kafin tsunduma cikin hannun masu aikata wannan ta'addanci.

1. Kauracewa sintiri da kai komo akan kari ba tare banbanta hanyoyin sufuri na shige da fice ba. Sauya hanyoyin zuwa da dawowa zai taimaka wajen rikitar da masu ta'adar garkuwa da mutane wajen rashin samun masaniyar kulla dabaru yayin neman cin galaba abin da suka nufata.

2. Sirranta al'amurran iyalai ko kuma 'yan uwa wajen kulla alaka a tsakanin sauran gama garin al'umma.

3. Gudanar da bincike mai zurfi yayin kulla alaka da al'umma musamman hadimai ko kuma abokanan hulda.

3. Domin kauce wa afka tarkon masu garkuwa da mutane, akwai bukatar mutum ya dauki rayuwa da sauki ta hanyar kankan da kai gami da rashin yin alfahari ko kuma wadaka da dukiya.

4. Samun kyakkyawar masaniya a kan makusanta, abokanan hulda da kuma makota musamman harkokin su na rayuwar ya da kullum.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Mataimakin shugaban kasa ya gana da masu sanya hannun jari a shirin habaka tattalin arziki na gwamnatin tarayya, NZESCO

5. Rashin kusanci tare da kauracewa saurin nuna yarda ko kuma amincewa da gama garin mutane masu baƙuwar fuska.

6. Sanya idanun lura da kuma kasancewa a ankare a koda yaushe kan al'amurran dake gudana a zamantakewa.

7. Kasancewa tare da wayar salula a koda wane lokaci domin bukatar gaggawa da gudun ko ta kwana.

8. Rashin yin gaggawa wajen yarda ko kuma amincewa da taimako na babu sididi babu sadada daga baƙuwar fuska da ba a santa ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel