Yanzu yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban mafarauta a Osun

Yanzu yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban mafarauta a Osun

- Masu garkuwa da mutane sun sace sarkin mafaruta na garin Ibokun, Amusa Olaleye Dunsin da wata mace guda daya

- An sace su na a ranar Litinin a bayan sun baro Esa Odo suna hanyarsu na zuwa Ilare

- Wannan na zuwa ne kwanakin kadan bayan masu garkuwa da mutane sun sace jami'an FRSC guda biyu

A yayin da jami'an tsaro ke kokarin ceto jami'an hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC da aka sace a hanyar Ilesha zuwa Akure a ranar Lahadi, an kuma sake sace wasu mutane biyu a ranar Litinin a karamar hukumar Obokun na jihar Osun.

Duk da cewa ba a gama tattaro cikaken baynai kan yadda aka sace su ba, Punch ta gano cewa mutane biyun sun baro Esa Odo ne suna hanyar zuwa Ilare a karamar hukuma Obokun lokacin da 'yan bindigan suka sace su.

Yanzu yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban mafarauta a Osun
Yanzu yanzu: 'Yan bindiga sun sace shugaban mafarauta a Osun
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

Kamar yadda rahoto ya nuna, wadanda aka sace sun hada da shugaban mafarauta na garin Ibokun, Amusa Olaleye Dunsin da wata mace mai suna Tayo da kuma wasu mutane uku da ke hanyarsu na zuwa Ilare a inda masu garkuwa da mutanen suka tare motarsu.

A yayin da masu garkuwa da mutanen su kayi nasarar awon gaba da Dunsin da macen guda daya, sauran fasinjojin uku sun tsere.

Dan majalisa mai wakiltan Obokun, Mr Tunbosun Oyinloye ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da kira ga wanda nauyin ya rataya a wuyansu su kawo karshen rashin tsaron da ake fama da shi a garin.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel