Duk budurwar da ta rasa mijin aure ta zo zan samo mata - Mustapha Soron Dinki

Duk budurwar da ta rasa mijin aure ta zo zan samo mata - Mustapha Soron Dinki

- A makon da ya gabata ne aka samu wata budurwa haifaffiyar Kano ta shiga shafin sada zumunta na Facebook ta bayyana cewar ita ba ta ga wata riba a aure ba, sai tsabar wahala

- Hakan ne yasa mutane musamman masu akidar addinin Musulunci suka yi mata caa a kai inda suke ganin maganar da ta yi ba ta dace ba

- Hakan ne ma ya sanya Mustapha Soron Dinki ya bayyana cewa a shirye yake ya samowa duk wata budurwa da ta rasa mijin aure miji mutukar ba ta sanya buri a rayuwarta ba

Karyar banza ce ki yi ta zama a gidanku kin saka burin sai dan gwamna, sanata ko kuma wani hamshakin mai kudi ya zo aurenki, kuma daga anyi magana sai ki ce babu mijin aure a gari.

Akwai mazaje da tarin yawa, suna nan buhu-buhu a ko ina a gari. Amma a ina matsalar take, matsalar ita ce irin burin da 'yammata suka sanyawa kansu shine ya saka da yawa daga cikin samari suka fita batun su, da yawa suka gwammace zuwa gidan kallon ball da wuraren debe kewa.

Wadanda suke da mutuwar zuciya a cikinsu sai suka koma auren jari. Kun ga kenan suma sun rama, don haka kowa sai jikinsa ya gaya masa, shi namiji babu mata ke kuma da kike jiran sanata babu miji domin kuwa sanatan da kike jira ba zai zo ba.

Duk budurwar da ta rasa mijin aure ta zo zan samo mata - Mustapha Soron Dinki

Duk budurwar da ta rasa mijin aure ta zo zan samo mata - Mustapha Soron Dinki
Source: Facebook

A shekarun da suka gabata, 'yammata sun gasawa maza aya a hannu a fannin soyayya, sai ka samu budurwa da samari kusan goma, kuma dukkaninsu so suke su aureta. Ita kuma ta na ta wahalar da su kamar kwallo.

To kuma kun san ance duniya rawar 'yammata, yau wanda ke gaba gobe sai kaga ya koma baya. Ba zan mance ba akwai wata budurwa dana sani, a lokacin har lissafa sunayen kalar motocin da ake zuwa gurinta da su take yi saboda tsabar buri da karya. Amma a karshe ba masu motar ne suka aureta ba, saboda kauye muka kai ta.

KU KARANTA: Babu wata riba a cikin aure sai wahala - Zainab Nasir Ahmad

Dama ita 'yar talaka bama a maganar ta, saboda yanzu yaran masu kudin ma fama suke da kansu. Mai karatu idan kana da lokaci shiga unguwannin GRA ko kaje Abuja kaga abin mamaki, sai ka iske mace ta kai shekara 40 a zaune a gidansu, kaga kenan ta zama sanatar gidansu.

Hakan ne zai sa kaga mace ta rame, ta lalace, saboda tsabar tunani. Ga kuma 'yan uwanki sun sako ki a gaba da maganganu na aure, saboda da yawa daga cikinsu sun gaji da ganinki a zaune a gida.

Wannan dalilin ne ya sanya wasu cikin damuwa har suke maganganu na kushe aure saboda miyagun dabi'unsu da kuma burin rayuwa. Ko sati ba a yi ba aka samu wata budurwa mai suna Zainab ta fito shafukan sada zumunta tana kushe aure, saboda ta rasa mijin aure.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel