An yanka ta tashi: Mutanen da aka kashe aka kone a Kaduna 'yan sanda ne ba masu satar mutane ba

An yanka ta tashi: Mutanen da aka kashe aka kone a Kaduna 'yan sanda ne ba masu satar mutane ba

A rahotannin da muka samu aa jihar Kaduna ya nuna cewa mutanen nan da fusatattun matasa suka kashe jiya da safe a tashar Kawo ba masu garkuwa da mutane ba ne, jami'an hukumar 'yan sanda ne

Idan ba a mance ba jiya majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton yadda wasu fusatattun matasa suka rufarwa wasu mutane a tashar Kawo inda suka kashe daya daga cikinsu sannan suka sanyawa motarsu wuta, kafin daga baya jami'an 'yan sanda su kawo musu dauki.

Abin ya kai ga an samu salwantar rai a cikin matasan da suka kama mutanen, yayin da jami'an 'yan sanda da sojoji suke kokarin ganin sun tarwatsa dandazon matasan. Bayan haka kuma wasu da yawa daga cikin matasan sun samu raunika a lokacin da matasan suka sanyawa motar mutanen wuta tare da mutum daya a cikin motar, inda daga baya aka gane cewa jami'in dan sanda ne da ya rako mutanen.

An yanka ta tashi: Mutanen da aka kashe aka kone a Kaduna 'yan sanda ne ba masu satar mutane ba
An yanka ta tashi: Mutanen da aka kashe aka kone a Kaduna 'yan sanda ne ba masu satar mutane ba
Source: Facebook

A wata sanarwa da Hakimin unguwar Kawon ya fitar, Mai Martaba Jibril Muhammad Magaji ya bayyana cewa wani abu ne ya hadasu da shi mutumin inda suka kama shi suka jefa a cikin motarsu, kuma tun daga jihar Legas suka biyo shi.

Hakimin ya ce lokacin da suka zo kama mutumin sai da suka je suka nemi izini a ofishin hukumar 'yan sanda, bayan an basu izini sai suka dunguma neman mutumin tare da wasu daga cikin jami'an 'yan sandan.

KU KARANTA: Hanyoyin da Dangote ya bi ya hana Ganduje tsige Sarkin Kano

Ga yadda bayanin Hakimin ya kasance:

"Ina mai yi muku barka da shan ruwa, sannan kuma ina so nayi amfani da wannan damar domin na jawo hankalin al'umma akan lamarin da ya faru yau a Kawo, bisa binciken da muka gabatar, gaskiyar magana mutanen da aka kashe, sannan kuma aka kona musu motarsu ba masu garkuwa da mutane ba ne.

Ya cigaba da cewa "Akwai wani muhimmin bayani da ke tsakanin su da shi (Alhaji Musa), kuma tun daga jihar Legas suke biye dashi tare da jami'an 'yan sanda, sannan da suka zo nan Kaduna sai da suka nemi izini a gurin hukumar 'yan sanda, bayan an basu izini shine suka fita nemansa."

A karshe dai Hakimin ya yi kira ga al'umma da su guji daukar doka a hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel