Da dumi dumi: Durbin Katsina, hakimin Jikamshi yayi murabus daga mukaminsa

Da dumi dumi: Durbin Katsina, hakimin Jikamshi yayi murabus daga mukaminsa

Guda daga cikin manya manyan masu rike da mukaman gargajiya a masarautar Katsina, mai girma Durbin Katsina, kuma hakimin Jikamshi, Alhaji Aminu Kabir Nagogo yayi murabus daga kujerarsa.

Aminu Kabir ya bayyana haka ne cikin wata wasika daya aika ma fadar Sarkin Katsina, zuwa ga mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayu, inda ya sanar dashi dalilin ajiye sarautar.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai hari cocin Kaduna, sun yi garkuwa da Fasto da yan mata 10

Da dumi dumi: Durbin Katsina, hakimin Jikamshi yayi murabus daga mukaminsa

Durbin Katsina
Source: UGC

Hakimin ya bayyana cewa babbar dalilinsa na ajiye wannan mukami shine saboda kwace sarautar durbin Katsina daga wajensa, inda aka tabbatar ma Sarkin Gabas, kuma hakimin Mani da sarautar Durbin Katsina.

Alhaji Aminu ya kara da cewa “Ina tunatar da Sarki da Yan majalisarsa cewa ni ban nemu sarautar Durbin Katsina ba, Maimartaba da kansa ya bani wannan sarauta saboda kauna, Allah ya saka da alheri, Yayi mana jagora dasakayya.

“Ina shaida maka ina godiya kwarai da gudunmuwar da aka bani a lokacin da nake Durbin Katsina, Hakimin Jikamshi, amma saboda wasu dalilai da shawara da nayi da Iyalina, Yan uwa, Masoya da abokan arziki naga ya dace in sadaukar da wannan jagoranci na Durbin Katsina Hakimin Jikamshi a karin kaina.” Inji shi.

Daga karshe Alhaji Aminu Kabir Nagogo ya yi fatan Allah Ya kawo dawwamammen zaman lafiya a masarautar Katsina, jahar Katsina da ma Najeriya gaba daya.

A wani labarin kuma Hakimin karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano, kuma Dan Galadiman Kano Haruna Sanusi, yayi murabus daga mukaminsa, bisa dalili na rashin lafiya da kuma sauyin tsarin masarauta da aka samu kwanan nan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel