Kungiyar Arsenal za ta bayar da 'yan wasa uku da kudi don daukan dan wasan Afrika

Kungiyar Arsenal za ta bayar da 'yan wasa uku da kudi don daukan dan wasan Afrika

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar Ingila ta nuna sha'awar bayar da 'yan wasan ta uku da kuma karin kudi domin daukan dan wasan gaba na kungiyar Crystal Palace kuma dan asalin kasar Ivory Coast dake nahiyar Afrika, Wilfred Zaha.

Zaha, mai shekaru 26, ya samu nasarar saka kwallo 10 a wasa 36 da ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace a kakar wasannin bana.

A karshen watan jiya ne Zaha ya sanar da cewar yana da sha'awar taka leda a gasar wasannin cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) a kakar wasannin badi, lamarin da ya tilasta Crystal Palace barin dan wasan ya tashi daga kungiyar.

An yi kiyasin cewar darajar Zaha na tsakanin Yuro miliyal 65 zuwa 80 - adadin kudin da ya yi daidai da tanadin da kungiyar Arsenal tayi domin sayen dan wasan gaba idan ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin UCL a kakar wasannin badi.

Kungiyar Arsenal za ta bayar da 'yan wasa uku da kudi don daukan dan wasan Afrika

Wifred Zaha
Source: Getty Images

Arsenal na fatan zuwa gasar UCL a kakar wasanni ta badi idan ta samu nasarar doke kungiyar Chelsea a wasan karshe da zasu buga a gasar cin kofin nahiyar Turai (UEFA) ranar Laraba mai zuwa.

Rahotanni sun bayyana cewar kungiyar Arsenal ta yiwa kungiyar Crystal Palace tayin ba ta 'yan wasa uku da kudi domin daukan dan wasa Zaha.

LABARAI MASU ALAKA: Ingila ce zalla wasan karshe na gasar cin kofin UCL da UL

UCL: Liverpool ta ga bayan Barcelona a wasan zagayen kusa da na karshe

Kungiyar tayi wannan tayin ne saboda ta rage yawan kudin da Crystal Palace ke nema a kan dan wasan. Kungiyar Crystal Palace ta kafe a kan cewar za ta sayar da Zaha ne kawai a kan farashin Yuro miliyan 80.

Yanzu dai Arsenal ta sanar da Crystal Palace cewar za ta bayar da 'yan wasan ta guda uku; Reiss, Nelson da Carl Jekinson, da kuma Yuro miliyan 40 domin Zaha ya koma Emirata da taka leda.

Babu wata babbar kungiyar kasar Ingila da ta nuna sha'awar daukan dan wasan, sai dai an bayyana cewar kungiyar PSG ta kasar Faransa da Dortmund ta kasar Jamus na sansana dan wasan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel