Babu wata riba a cikin aure sai wahala - Zainab Nasir Ahmad

Babu wata riba a cikin aure sai wahala - Zainab Nasir Ahmad

- Wata matashiya 'yar Kano ta fita shafinta na sada zumunta ta bayyana ra'ayinta akan aure

- Inda ta bayyana cewa babu wata riba a cikinsa sai wahalar rayuwa

A lokacin da mafi yawancin iyaye suke ta faman Allah-Allah wurin ganin su tura 'ya'yan su mata dakin mazajensu domin gujewa yaran fadawa sharrin zamani wurin lalacewar tarbiyya, sai kwatsam wata budurwa mai amfani da shafin yanar gizo na Facebook, mai suna Zainab Naseer Ahmad, ta bayyana cewa mutane ne kawai suke ta faman zuzuta sai kace akwai wata babbar nasara da jin dadi a ciki, kuma a zahirin gaskiya wannan tunanin na mutane shirme ne kawai da rashin sannin inda duniya ta sa gaba, kai hasalima babu wani abin jin dadi a cikin sa.

Babu wata riba a cikin aure sai wahala - Zainab Nasir Ahmad

Babu wata riba a cikin aure sai wahala - Zainab Nasir Ahmad
Source: Facebook

Ta kara da cewa "Iyaye da mutane sai su yi ta takura yarinya idan ta kai minzalin aure batayi ba, hakan ma sai ya sanya kaga wasu mazan marasa tunani suna ganin kamar idan sun aureki sunyi miki alfarma ne."

A cewarta, "shi fa auren nan abu ne guda daya kacal a rayuwa, sannan kuma ba kowane mutum da aka halitta ne zai yi shi ba, ta kara da cewa gaskiya ya kamata iyaye da mutane su dai na musgunawa mata akan cewa dole sai sunyi aure."

KU KARANTA: Yadda wani jarumin kare ya ceto rayuwar wani jariri da aka binne da rai

Ta kuma kara da cewa, wasu matan suna ganin idan sunyi aure sun fi wadanda basu yi ba, ba haka bane, duk daya suke.

Daga karshe ta kara jaddada manufarta ta cewa babu shakka babu wani abin azo a gani a cikin auren da kowa yake ta faman kwallafa rai akai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel