Yan bautar kasa ma za su samu sabon albashi – Zainab Ahmed

Yan bautar kasa ma za su samu sabon albashi – Zainab Ahmed

Zainab Ahmed, ministar kudi, ta bayyana cewa masu yiwa kasa hidima za su samu sabon albashi a matsayin alawus.

Da take Magana a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu yayin da take jawabi ga manema labarai kan ayyukan ma’aikatar ta, Zainab tace gwamnatin tarayya na aiki domin daidaita sabon albashi.

“Baya ga Karin mafi karancin albashi daga N18,000 zuwa N30,000, akwai wasu yan gayer-gyare da ya zama dole mu tattauna da kungiyoyin kwadago,” inji ta.

“Za a kammala kmai ne bayan tattaunawar sannan hakan zai sa a san nawa za a kara wa sauran ma’aikata da ke karban sama da mafi karanin albashi.

Yan bautar kasa ma za su samu sabon albashi – Zainab Ahmed
Yan bautar kasa ma za su samu sabon albashi – Zainab Ahmed
Asali: UGC

“Yana iya asancea kudi daya ko kuma gwargwado, amma dai sauran bangaren da ke a bayyana shinecewa za a kara albashin yan bautar kasa suma saboda, bisa dokar shine suma su samu akalla mafi karancin albashin sannan ya zama dole NYSC ta karu zuwa N30,000.

KU KARANTA KUMA: An kai farmaki sakatariyar APC, an sace takardu, na’urar sanyaya wuri, talbijin da sauransu

“Don haaka, saboda bamu gama tattaunawa da kungiyar kwadago ba, ba zan iya bayar da cikakken jawabi kan aikin ba saboda ana kan aiki a kai.”

Ministar kudin ta kuma sanar da cewa za a rarraba naira biliyan N649.43 ga gwamnatocin jiha a matsayin kudin karshe na Paris Club.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel