Dalilai 6 dake hana matasa aure a Najeriya

Dalilai 6 dake hana matasa aure a Najeriya

Bayan wani bincike da masana suka yi a Najeriya domin gano dalilan da suka sanya aure ke yiwa samari wahala a kasar, binciken ya nuna cewa yawancin samarin wannan lokacin sun fi kaunar su zauna a matsayin gwauraye da suje suyi aure

A yadda samarin ke gani hakan shine mafita, saboda ba su ba shiga matsalolin da suke gani ma'aurata suna shiga tsakaninsu da matayensu.

'Yan jarida sun yi magana da wasu gwauraye da suke zaune a babban birnin tarayya Abuja, inda suka bayyana dalilansu na kin yin aure.

Dalilai 6 dake hana matasa aure a Najeriya
Dalilai 6 dake hana matasa aure a Najeriya
Source: Depositphotos

Wasu daga cikin manyan dalilan da suka sanya samari ba su son yin aure sun hada da:

1. Talauci: - Kullum kukan da mutane ke yi musamman matasa shi ne rashin aikin yi ko sana'a, kuma sun dauki hakan a matsayin babban dalilin da ya ke hana su yin aure.

2. Rashin gaskiya tsakanin masoya: - A wannan fannin dai babu wani mai gaskiya tsakanin saurayi da budurwar. Domin kuwa dukkanin su karya suke yiwa junansu, kuma daga baya idan suka gano gaskiyar lamari sai soyayyar ta gagara har su zo su rabu ma.

3. Banbancin Al'ada: - Saboda banbancin al'ada ya kan sanya wasu masoyan rabuwa da juna, saboda ba za su iya hakuri da wasu al'adu na bangaren budurwa ko saurayi ba.

KU KARANTA: Yadda kotu ta raba auren wani limami da ke kwanciya da 'ya'yan cikinsa guda uku

4. Addini: - Addini yana da matukar tasiri a soyayya, domin kuwa idan aka samu banbancin addini a soyayya mafi yawancin soyayyar da ake yi tana zuwa karshe, kuma ba wai saboda ba su son junansu ba ne.

5. Yaudara tsakanin masoya: - Mafi yawanci masoya sukan jima suna soyayya da juna cikin yaudara. Hakan yafi faruwa ga mata. Sai kaga mace na kaunar saurayinta tsakani da Allah, ashe shi kuma yana can ya tara wasu 'yan matan daban. Kuma zaka ga cewa shi tun asali ma ba aure ne ya kai shi wurinta ba. Sai bayan tafiya ta yi nisa sai kaga masoyan sun rabu suna yiwa juna Allah ya isa.

6. Wayewa: - Wayewa da ta shigo cikin al'umma yanzu ita ce ummul aba'isin rugujewar tarbiyar yaran mu a wannan lokacin. Shaye-shaye da zinace-zinace ya zama ruwan dare a ko ina, zaka ga yarinya karama idon ta ya bude akan rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel