Wani mutumi ya roki manyan Arewa su hana al'adar Hausawa ta aurar da yara kanana

Wani mutumi ya roki manyan Arewa su hana al'adar Hausawa ta aurar da yara kanana

- Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun jima suna korafi akan yawan aurar da yara mata kanana da ake yi a yankin arewacin Najeriya musamman Hausawa wanda suka dauki abin tamkar al'ada

- Wani mutumi mai kishin yankin arewa ya fito ya roki shugabanni da malaman addini na arewa akan su sanya baki wurin kawo karshen aurar da yara matan

Wani mutumi musulmi ya yi magana game da auren wuri da ake yiwa yara kanana a arewacin Najeriya, sannan ya roki shugabanni da Malaman addinin Musulunci da su sanya baki akan matsalar.

Mutumin mai suna Umar Ibrahim ya wallafa sakon a shafinsa na Twitter:

Wani mutumi ya roki manyan Arewa su hana al'adar Hausawa ta aurar da yara kanana
Wani mutumi ya roki manyan Arewa su hana al'adar Hausawa ta aurar da yara kanana
Asali: UGC

"Ina so na roki manyan arewa da malamai, don Allah su fara magana akan auren wuri da ake yiwa yara kanana a arewacin kasar nan. Abin babu dadi ko kadan idan naga yarinya karama da goyo a baya idan na tambaya dan waye sai ace mini nata ne."

KU KARANTA: Labaran Kannywood: Mahaifiyata ta ce duk wanda ya sake zagina na rama ba ta yafe mini ba - Adam Zango

Ya cigaba da cewa: "Na taba tambaya a wani asibiti kuma aka fada mini cewa wannan ba komai ba ne. Wannan ba addini ba ne, al'adace kawai irin ta Hausawa, kuma ba al'ada ba ce mai kyau. Gwanda na zauna banda aure da ace na auri yarinya karama. Ina mai bada shawara ga duk wanda yake da kanwa wacce aka yi mata aure ta na da shekaru kasa da 16, ya gudu da ita."

Ya cigaba da cewa: "Mazan za su aure su, suyi mata ciki sai su sake ta, wasu ma har da 'ya'ya ake sako su, a karshe dai za ta zo ta shiga halin da ba bu wanda yake so ya ga dan uwanshi ya shiga. Gasu nan a ko ina suna yawo kowa yana ganinsu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel