Maki 370 na kudirta zan samu - Dalibin da ya fi kowa samun nasara a jarabawar JAMB ta bana
Mai shekaru goma sha biyar, Ekene Franklin, hazikin dalibi da ya fi kowa samun nasara a jarabawar neman shiga jami'a ta hukumar JAMB wanda samu maki 347, ya yi furuci dangane da dalilin wannan gagarumar nasara da ya samu.
Duk da cewar ya yi matukar farin ciki, Ekene wanda ya kasance dalibin aji shida a makarantar sakandire ta Meiran Community School da ke wajen gari a jihar Legas, ya bayyana cewa ya kudirta samun maki 370 cikin 400 da hukumar JAMB tayi tanadi.
Da ya ke ganawa da manema labarai na jaridar The Nation, Ekene yayin bayyana yadda ya shiga cikin dimuwa ta farin ciki ta abin yabo da yayi, ya jingina nasarar sa da yawaita shiga gasar zakakuraci a tsakanin dalibai da gwamnatin jihar Legas ke shirya wa.
KARANTA KUMA: Yaki da rashawa: Har yanzu mu na da tafiya mai nisan gaske - Osinbajo
Mahaifiyar sa Misis Chinelo Ezeunala, wadda ta kasance malamar darasin Chemistry a makarantar Hightree College, ta bayyana farin ciki matuka a sanadiyar bajintar da dan ta yayi a duk fadin Najeriya.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng