Za’a kashe N4,068,000,000 wajen tarbar zababbun yan majalisun dokokin Najeriya 469

Za’a kashe N4,068,000,000 wajen tarbar zababbun yan majalisun dokokin Najeriya 469

Kimanin naira biliyan hudu da miliyan sittin da takwas (4,068,000,000) ne za’a rarraba ma kafatanin zababbun yan majalisun dokokin Najeriya, sababbi da masu maimaita a matsayin kudin maraba, da zarar an rantsar dasu a watan Yunin shekarar 2019.

Wannan bayani ya fito ne daga wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa bayan wani zuzzurfan bincike data gudanar game da majalisa, wanda ya nuna cewa ana biya duk wani sabon dan majalisa wadannan kudade ne domin ya samu wurin zama dana kayan daki..

KU KARANTA: Angulu ba zata koma gidanta na tsamiya ba – Inji gwamnan APC daya koma PDP

Za’a kashe N4,068,000,000 wajen tarbar zababbun yan majalisun dokokin Najeriya 469

Majalisar wakilai
Source: Twitter

Bayanai daga hukumar rarraba arzikin kasa, RMAFC, ya nuna cewa ana biyan yan majalisu kudin wurin zama sau daya a duk shekara, yayin da ake biyansu alawus na kudin kayana daki sau daya a shekara daya.

Kudin da dokokokin RMAF na 2007 ta tanadar a biya duk wani majalisar wakilai na wadannan alawus alawus din shine naira miliyan tara da dubu dari tara da shirin da shida da sittin da biyu da kwabo 5 (N9,926,062.5), haka zalika sune alawus din da za’a biya sabon Alkali.

Yayin da takwaransa na majalisar dattawa doka ta tanadi a biyashi naira miliyan goma da dubu dari da talatin da biyu (N10,132,000)a matsayin alawus din gida dana sayen kayan daki.

Za’a kashe N4,068,000,000 wajen tarbar zababbun yan majalisun dokokin Najeriya 469

Majalisar dattawa
Source: UGC

A jimlace akwai yan majalisar wakilai 360, zasu samu naira biliyan uku da miliyan hamsin da bakwai kenan (N3,057,000,000) yayin da Sanatocin Najeriya 109 zasu samu naira biliyan daya da miliyan dari da hudu da dubu dari uku da tamanin da takwas (N1,104,388,000).

Game da kudin sayen mota kuwa, kowanni Sanata zai samu naira miliyan takwas da dubu dari da biya da dari shida (N8,105,600) yayin da dan majalisar wakilai zai samu naira miliyan bakwai da dari tara da arba’in da dari takwas da hamsin (N7,940,850), sai dai hukumar RMAFC tace wannan kudin bashi ake bayarwa.

Daga cikin sauran kudaden da ake biyan yan majalisa a duk wata akwai kudin sayen mai a gyaran mota kashi 75 na albashinka, kudin bushasha kashi 30 na albashinka, kudin wuta da ruwa kashi 30 na albashinka, kudin jarida kashi 15 na albashinka, kudin sayen kaya kashi 25 na albashi, kudin gyaran gida kashi 5 na albashi, da kuma kudin aikin mazaba kashi 250 na albashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel