Madalla: Al’umman jihar sokoto sun samu ruwan sama na farko

Madalla: Al’umman jihar sokoto sun samu ruwan sama na farko

- Alhamdulillah al'umman garin Sokoto sun samu ruwan damuna na farko ya sauka a yankin

- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da zafi da rana yayinda masu azumi kan shiga wani yanayi saboda kishir ruwa

- Saukar ruwan saman ya haifar da farin ciki da jin dadi a zukatan jama'a, yayinda kananan yara ke ta rawa, suna waka da tafa hannu a cikin ruwan saman wanda ya zo da guguwar iska da kasa

Mazauna birnin Sokoto da dama sun samu saukin yanayi sosai a ranar Litinin bayan ruwan damuna na farko ya sauka a yankin.

An fara ruwan saman ne 6pm da yan mintuna kuma an kwashe kusan sa’a guda ruwan na zuba kamar da bakin kwarya.

Ruwan saman ya tsaya ne a daidai lokacin da al’umman Musulmi ke shirye-shiryen bude baki na azumin da suka yi a wannan rana.

Madalla: Al’umman jihar sokoto sun samu ruwan sama na farko
Madalla: Al’umman jihar sokoto sun samu ruwan sama na farko
Asali: Depositphotos

Ruwan damunan ya sauka ne a yayinda mazauna yankin ke gwagwarmaya da yanayin zafi da ake fama dashi yan kwanakin nan.

KU KARANTA KUMA: Shugaban karamar hukuma a Katsina ya koka akan lamarin tsaro

An gano mutane da dama na ta farin ciki da murna kan sauyi da saukar ruwan ya kawo.

An gano kananan yara na ta rawa, suna waka da tafa hannu yayinda suke rawa a cikin ruwan saman wanda ya zo da guguwar iska da kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel