Majalisar wakilai za ta binciki CBN, ma'aikatar kudi da 'First Bank'

Majalisar wakilai za ta binciki CBN, ma'aikatar kudi da 'First Bank'

Majalisar wakilai ta dora wa kwamitin ta na kula da harkokin kwangila alhakin gudanar da bincike a kan zargin wasu hukumomi da saba ka'idar gwamnati wajen bayar da wata kwangilar sayen kayan aikin noma.

Mambobin majalisar sun umarci kwamitin ya binciki babban bankin kasa (CBN), ma'aikatar kudi da 'First Bank' a kan zargin saba ka'ida wajen bayar da kwangilar sayen kayan aikin noma ga gwamnatin jihar Oyo.

'Yan majalisar sun bayyana bayar da kwangilar a matsayin cin dunduniyar kokarin gwamnatin tarayya na wadata Najeriya da abincin da aka noma a cikin kasa.

Majalisar ta bayar da umarnin ne a karkashin matsalolin dake bukatar kulawar gaggawa.

A wani kudirin mai alaka da wannan, majalisar ta bukaci kwamitin ya binciki zargin saba ka'ida wajen bayar da kwangila da jami'ar Lgas tayi

Ana zargin mahukuntar jami'ar da suka gabata da masu ci a yanzu da kuma kwamitin gudanarwar ta da hannu a cikin saba ka'idar bayar da kwangilar.

An bawa kwamitin wa'adin kwanki biyar domin gabatar da cikakken rahoton bincike a gaban majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel