Gaskiyar labarin da ke nuna cewa Yusuf Buhari ya mallaki dala biliyan 2.3

Gaskiyar labarin da ke nuna cewa Yusuf Buhari ya mallaki dala biliyan 2.3

- Kwanakin baya an dinga yada wata jita-jita da ke nuna cewa Yusuf Buhari shi ne na hudu a cikin jerin 'ya'yan shugaban kasada suka fi kowa kudi aduniya

- A bayyana cewa ya mallaki dala Amurka biliyan 2.3

A kwanan nan an rika yada wata jita-jita dake da dangantaka da mujallar Forbes inda aka bayyana cewa ta ba da rahoton Yusuf Buhari, wato dan gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne a matsayin mutum na hudu a 'ya'yan shugabannin kasashen duniya da suka fi kowa kudi.

Rahoton ya bayyana cewa Yusuf Buhari ya mallaki dala biliyan 2.3.

Al'umma musamman a kafar sada zumunta na zamani sun dinga sanya labarin a shafukansu na Facebook, Twitter da kuma Instagram, kuma an bayyana cewa labarin ya samo tushe daga wasu kafafen yada labarai na Najeriya.

Gaskiyar labarin da ke nuna cewa Yusuf Buhari ya mallaki dala biliyan 2.3
Gaskiyar labarin da ke nuna cewa Yusuf Buhari ya mallaki dala biliyan 2.3
Asali: UGC

Menene gaskiyar wannan lamarin?

A wani bincike da wata kafar yada labarai ta AFP ta gabatar ta binciko cewa labarin ba shi da asali, kuma ta tabbatar da cewa mujallar Forbes ba ta ruwaito rahoto makamancin haka ba.

Hakazalika binciken da kafar yada labarai ta BBC ta gabatar ya nuna cewa labarin ba shi da tushe bare makama, domin kuwa babu wata kafa da ta bada rahoton haka.

KU KARANTA: Sama da mutane dubu 500 ne suka cika aikin Kwastan

Mujallar Forbes ta ruwaito jerin manyan masu kudin Afirka a wannan shekarar ta 2019, inda ta bayyana 'yan Najeriya mutum hudu kawai, kuma duk ciki babu Yusuf Buhari a ciki.

Na daya shine Alhaji Aliko Dangote, wanda ya mallaki dala biliyan 10.3, sai Mike Adenuga wanda yake da mallakin dala biliyan 9.2 a matsayin na biyu, na uku shine Abdulsamad Rabiu (wanda ya ke da kamfanin siminti na BUA) shi kuma ya mallaki dala biliyan 1.6.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel