An fara ruguje gidan casu a Abuja

An fara ruguje gidan casu a Abuja

Gwamnati ta bada umarnin ruguje gidan rawan nan mai suna Caramelo, dake babban birnin tarayya Abuja, inda 'yan sanda suka kama 'yammata da yawa da su ke zargin su da karuwanci

Gwamnatin babban birnin tarayya Abuja ta ruguje gidan rawan nan mai suna Caramelo Lounge, da ke Abuja, makonni kadan bayan hukumar 'yan sanda sun kama mata da suka yi zargin cewa karuwai ne a babban birnin tarayyar.

A safiyar jiya Litinin ne, motar ruguza gini, wacce aka fi sani da 'Bulldozer' a turance ta isa inda gidan rawar ya ke, a bisa umarnin gwamnatin babban birnin tarayyar, inda ta fara ruguje gidan rawar ba tare da bata lokaci ba.

An fara ruguje gidan casu a Abuja
An fara ruguje gidan casu a Abuja
Asali: Facebook

Idan ba manta ba majiyar mu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton yadda hukumar 'yan sanda suka kama 'yammata a gidajen rawa aAbuja, inda suke zarginsu da aikata karuwanci.

To sai dai 'yammatan su ma sun zargi jami'an 'yan sandan da yi musu fyade a lokacin da suka kamo su din, inda suka bayyana cewa sun dinga amfani da duk wata wacce bata da kudin da za ta basu cin hanci. Hakan ne ya kawo kace-nace a cikin al'umma musamman ma ga kungiyoyin lauyoyi dana kare hakkin dan adam.

KU KARANTA: Garin dadi ba kusa ba: Wani sarki ya saka doka akan mazajen kasarsa da su dinga auren mata a kalla guda hudu

Hukumar 'yan sanda ta kasa ta sha alwashin hukunta duk wani jami'i da ta kama da laifi a zargin fyaden da 'yammatan suke yi.

Ba wannan karo na farko da aka fara samun jami'an 'yan sandan da laifi makamancin haka ba, a lokuta da dama sukan harbi mutum ko su dake shi, inda suke bayyana hakan a matsayin tsautsayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel