Salah, Mane, da Aubameyang sun fi kowa kwallaye a Firimiya

Salah, Mane, da Aubameyang sun fi kowa kwallaye a Firimiya

‘Yan wasan kwallon kafa 3 ne su ka karbi kyautar yawan kwallaye a kakar wasan bana a Ingila. Pierre-Emerick Aubameyang, da Mohammed Salah da kuma Sadio Mane ne su kayi fice a Gasar BPL.

‘Yan wasan na Liverpool har 2 ne su ka samu kyautar takalmin gwal da ake ba wanda ya fi kowa zura kwalla a duk shekara. Mohammed Salah da Takwaransa Sadio Mane sun zura kwallaye har 22 ne a kakar shekarar nan na bana.

Haka zalika ‘dan wasan Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, ya samu cin kwallaye 22 a shekarar na 2018/19. Wannan ne dai karon farko da ‘yan wasa 3 su ka raba wannan kyauta a Gasar Firimiya tun bayan da haka ya faru a 1998.

KU KARANTA: Wasannin da su ka taimakawa Man City wajen cin Firimiya

Salah, Mane, da Aubameyang sun fi kowa kwallaye a Firimiya
Babban 'Dan wasan Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang
Source: Getty Images

A shekarar 1998/99 ne aka samu Jimmy Floyd Hasselbaink, Michael Owen da kuma Dwight Yorke suka taru su ka lashe kyautar takalmin na gwal bayan sun zama ‘yan wasan da su ka fi kowa yawan kwallaye a Gasar Firimiya na kasar Ingila.

Abin da ya bada sha’awa wannan karo shi ne dukkanin wadannan ‘yan kwallo watau Emerick Aubameyang, da Mohammed Salah da Sadio Mane sun fito ne daga Afrika. ‘Yan kwallon sun yi wa Afrika abin alfahari a kasar Turan.

‘Dan wasa Aubameyang ya zura kwallaye 2 ne a raga a wasan Arsenal na karshe da Burnley. Haka zalika Sadio Mane ya ci kwallaye 2 a kan 20 din da yake da su a da. Salah wanda ya buga wasan karshe ya kare kakar ne shi ma da kwallaye 22.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel