Yadda Bindow da makarraban sa ke watandan kadarorin jihar Adamawa – Fintiri ya koka

Yadda Bindow da makarraban sa ke watandan kadarorin jihar Adamawa – Fintiri ya koka

Yayinda ake shirye-shiryen rantsar da sabbin gwamnatoci a ranar 29 ga watan Mayu, zababben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya koka akan yadda gwamnan jihar mai barin gado, Jibrilla Bindow da ayarinsa ke watanda da arzikin jihar.

Kwamitin shirya mika mulki na bangaren zababben gwamna Fintiri ne suka koka da lamarin.

Jagoran kwamitin, John Yahaya ya bayyana cewa a dan kwanakinnan sai gashi gwamnatin jihar na ta bada kwangiloli masu yawa sannan ta na biyan su cif tun ba a yi su ba.

Bayan haka gwamnatin na raba wa makarrabanta wasu daga cikin kadarorin jihar ba tare da an bi doka ba.

Yadda Bindow da makarraban sa ke watandan kadarorin jihar Adamawa – Fintiri ya koka
Yadda Bindow da makarraban sa ke watandan kadarorin jihar Adamawa – Fintiri ya koka
Asali: UGC

“Sannan kuma tuni har gwamna Bindow ya biya kansa kudin sallama bayan ga dubban ma’aikatan jihar da bai-iya biyan su albashi ba duk da shiga watan Ramadana da aka yi.

“Kuma tun kafin a shirya yadda za a biya sabon tsarin albashi sai gashi har ya bayyana cewa jihar zata biya sannan kuma yana ta daukan sabbin ma’aikatan da bai dauka ba a da."

KU KARANTA KUMA: Yan daba sun tarwatsa masu zanga-zangan nuna rashin goyon bayan raba masarautar Kano

Sai dai kuma, kakakin gwamnatin jihar, Ahmed Sajoh, ya karyata zargin inda yake cewa babu kamshin gaskiya a ciki.

Sajoh ya karyata haka sannan ya ce gwamnati ba za ta yi abinda ba haka ba har zuwa ta fice daga gidan gwamnati ranar 29.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku latsa domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel