Da duminsa: An kashe mutane bakwai, an kone daruruwan gidaje a jihar Taraba

Da duminsa: An kashe mutane bakwai, an kone daruruwan gidaje a jihar Taraba

- An kashe mutane bakwai a wani hari da 'yan bindiga suka kai jihar Taraba

- Rahotanni sun nuna cewa an nema mutane da yawa an rasa, bayan 'yan bindigar sun sanyawa kauyukan da suka kai harin wuta

An bada rahoton kashe mutane bakwai a Rafin Kada da Kente a garin Jukun cikin karamar hukumar Wukari jihar Taraba, yayin da aka kai wani mummunan hari da safiyar Jumaa'ar da ta gabata.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa mutane da yawa sun bace, yayin da daruruwan gidaje suka kone.

Wadanda suka kai harin ana zargin cewa 'yan bindigan kabilar Tiv ne, sun kuma kori sauran al'ummar kauyukan yankin kusa da Rafin Kada_Donga da Takum.

An kai harin ne makonni kadan bayan kabilar Tiv da ke jihar Taraba sun ki amincewa da bukatar zaman lafiya da gwamnatin jihar ta Taraba ta hada wata kwamiti domin kawo karshen rikicin da ke addabar mutanen jihar musamman ma kabilar Tiv da Jukun.

Da duminsa: An kashe mutane bakwai, an kone daruruwan gidaje a jihar Taraba

Da duminsa: An kashe mutane bakwai, an kone daruruwan gidaje a jihar Taraba
Source: Original

Wani shaida a yankin Mista James Agbo ya bayyanawa Aminiya cewa wadanda suka kai harin sun shigo garuruwan da manyan bindigogi inda suka tarwatsa dukkanin al'ummar garin.

Mutumin ya bayyana cewa da yawan mutane sun fita daga garuruwan da raunuka a jikinsu, inda daruruwan mutane da suka hada da mata da yara har yanzu ba a san inda suke ba.

Shugaban karamar hukumar Wukari, Mista Adigrace Daniel ya bayyanawa manema labarai a wayar salula cewa an kashe mutane biyar a Rafin Kada yayin da aka kashe mutane biyu a garin Kente.

KU KARANTA: 'Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi

Shugaban ya bayyana cewa mutanen da suka ji rauni yanzu haka an garzaya da su asibiti domin karbar magani.

Ya yi zargin cewa kabilar Tiv ne suka kai hari kauyukan kabilar Jukun a ranar Juma'a da safe.

Mista Adigrace Daniel ya bayyana cewa mutane da yawa sun bace a lokacin da 'yan bindigar su kai hari kauyukan.

Da aka kira jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar bai samu damar daukar wayar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel