Shariff Rabiu Usman Baba: Muhimman batutuwa 10 game da rayuwarsa
Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, da sanyin safiyar Alhamis, 9 ga watan Mayu wanda yayi daidai da 4 ga watan Ramadan Allah Ya yi ma fitaccen sha'irin nan mai wakokin begen Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Sherif Rabiu Usman Baba rasuwa.
Da wannan ne Legit.ng ta kawo musu wasu muhimman bayanai game da wannan bijimin mawakin bege dan asalin jahar Kano daya shahara musamman a tsakanin shekarun 1980 zuwa 2000, kamar haka;
KU KARANTA: Ke duniya! Uwargida ta hada baki da kwartonta sun kashe mijinta
- A shekarar 1965 aka haifi Shariff Rabiu Usman Baba
- Dan asalin unguwar Gwammaja ne, amma yana zama a Janbulo
- Shine shugaban kungiyar masu bege ‘Shu’ara’ul Islam’
- Shi ya fara zamanantar da wakokin bege da kade kade
- Shekarunsa 54 Allah Yayi masa rasuwa
- Rabiu Baba yayi fama da ciwon kafa wanda yayi ajalinsa
- Da Asubahin ranar Alhamis ya rasu
- Ya rasu yana da Mata 4
- Ya rasu ya bar yaya 18
- Da yammacin Alhamis aka yi jana’izarsa a unguwar Gwammaja
A zamaninsa, marigayi Rabiu Usman Baba ya ciri tuta wajen rera wakokin yabo ga Manzon Allah da Iyalansa, Wasu daga cikin fitattun wakokinsa sun hada da Tauhidi Babu tantama, Mutuwa, Tsumagiya, Sha yabo, Majalisi, Wakar Sadiya, Zumunci, Tambaya, Sharifai, Fadima, Garkuwa, Batijaniya, Bakadiriya, Fiyayya, Sayyadil Wara da Zuma.
Har zuwa yanzu jama’a da dama na cigaba da bayyana alhininsu game da mutuwar babban sha’irin, tare da jimamin rashinsa, musamman duba da yadda wakokinsa suka yi tasiri a tsakanin mabiya darikar Tijjaniyyah da Kadiriyya.
Da fatan Allah Ya jikansa da gafar, da dukkanin Musulman da suka rigamu gidan gaskiya, Amin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng