Kowa ya samu rana yayi shanya: Ganduje ya nada sabon Alkalin Alkalai a jahar Kano

Kowa ya samu rana yayi shanya: Ganduje ya nada sabon Alkalin Alkalai a jahar Kano

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nada mai sharia Nura Sagir a matsayin sabon Alkalin Alkalan jahar Kano, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sagir ya kwashe tsawon shekaru hudu yana rike da wannan mukami amma a matsayin mukamin rikon kwarya, har sai a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu da gwamnan ya tabbatar dashi.

KU KARANTA: EFCC ta cafke dan majalisa akan laifin damfara Malaman makaranta naira miliyan 4

Dayake jawabi a fadar gwamnatin jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana sabon Alkalin Alkalan a matsayin mutumin da yayi suna wajen jajircewa a bakin aiki, tare da nuna kwarewa da kokari a duk aikin daya sanya a gaba.

Haka zalika gwamnan ya shawarci sabon Alkalin Alkalan daya zage damtse tare da karkatar da hankalinsa wajen ganin ya samar da tsarin da zai gaggauta kammala sharia tare da yanke hukuncin adalci cikin kankanin lokaci.

Bugu da kari gwamnan yace gwamnatinsa zata cigaba da hada kai da bangaren sharia don ganin ta inganta sha’anin walwalar ma’aikatan sharia, tare da samar musu da yanayin aiki mai kyau.

Shima a nasa jawabin, Alkali Sagir ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Ganduje bisa amincewa da yayi da cancantarsa ta nadashi wannan mukami, sa’annan yayi alkawarin rike amanar rantsuwar aiki daya dauka.

Daga karshe sabon jojin ya bukaci gwamnan jahar Kano daya kara nada wasu sababbin Alkalai a kotunan jahar domin ta haka ne kadai za’a iya gaggauta kammala shari’u tare da yanke hukuncin adalci cikin kankanin lokaci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel