Liverpool V Tottenham, Chelsea V Arsenal: Ingila ce zalla wasan karshe na gasar cin kofin UCL da UL

Liverpool V Tottenham, Chelsea V Arsenal: Ingila ce zalla wasan karshe na gasar cin kofin UCL da UL

A karo na farko a tarihin kwallon kafa, kulob din kasar Ingila hudu zasu fafata a wasan karshe na gasar cin kofunan nahiyar turai; gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) da kofin nahiyar Turai (UL).

Za a fata a wasan karshe na gasar UCL tsakanin kungiyar Liverpool da takwararta Tottenham, za a buga wasan ne a brnin Madrid na kasar Spain.

A gasar UL, za a fafata tsakanin kungiyar Chelsea da takawararta Arsenal a wasan karshe da za a buga a ranar 27 ga watan Mayu.

Liverpool V Tottenham, Chelsea V Arsenal: Ingila ce zalla wasan karshe na gasar cin kofin UCL da UL

'Yan wasan Arsenal yayin murnar zira kwallo a ragar Valencia
Source: UGC

Liverpool ta doke kungiyar Barcelona ta kasar Spain a wasan zagayen na kusa da na karshe, yayin da kungiyar Tottenham ta doke kungiyar Ajax ta kasar Netherlands.

DUBA WANNAN: UCL: Liverpool ta ga bayan Barcelona a wasan zagayen kusa da na karshe

Chelse ta samu nasarar zuwa wasan karshe a gasar UL bayan ta samu nasara a kan kungiyar Frankfurt ta kasar Jamus a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Kungiyar Arsenal ta kai ga wasan karshe a gasar UL bayan samun gagarumar nasara a kan kungiyar Valencia ta kasar Spain.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel