Wani mutumi ya saki matarshi kwana daya bayan daurin aurensu

Wani mutumi ya saki matarshi kwana daya bayan daurin aurensu

- Wani mutumi ya yiwa matarsa saki uku, kwana daya da yin aurensu, bayan ya gano cikon da take yi a bayanta a lokacin da yaje kwanciya da ita

- Mutumin ya ce bayan matar tasa yana daya daga cikin abinda ya ja hankalinsa ya aureta

- Ya kuma bayyana cewa sun yi kokarin su kauracewa zina a lokacin da suke soyayya, shine kuma dalilin da yasa ya kasa ganewa tun da farko

Wani mutumi dan kasar Ghana yana tunanin sakin matarsa, bayan aurensu da bai wuce awa 24 da daurawa ba.

Mutumin ya fara tunanin sakin matar tasa ne, wadda ya aureta kwana daya da ya wuce, saboda ya fahimci cewa siffar matar da yake tuanin ya aura ba ita ya gani ba lokacin da yaje kwanciya da ita.

Wani mutumi ya saki matarshi kwana daya bayan daurin aurensu
Wani mutumi ya saki matarshi kwana daya bayan daurin aurensu
Asali: Facebook

A bayanin da mutumin da ya yi lokacin da yake bayyana jimanin sa ga wani masani a fannin zamantakewa mai suna David Papa Bondze-Mbir, sunyi alkawarin ba za su taba kwanciya da juna ba har sai bayan sunyi aure.

Ya ce a lokacin da suke soyayya ya san matar tashi da siffa wacce kowanne mutum ya gani zai ji sha'awa, kuma siffar ta ne yasa yaji zai iya aurenta.

KU KARANTA: Ashe jami'an 'yan sandan dake jihar Lagos kasuwanci suke zuwa yi ba aiki ba

Amma a daren su na farko, lokacin da suka yi niyyar kwanciya irin ta aure, ya yi mamakin yadda aka yi siffar jikin matar tashi ya canja, maimakon da yana ganin komai lafiya lau sai yaga cewa ba haka take yi ba.

Ya bayyana cewa dama shi bayan matar tashi ne yasa yaji yana sonta, kuma sai gashi yanzu ya gano cewa ciko take yi, ba asalin siffarta ba ce ashe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel