Jama’tu Nasril Islam ta koka ga Buhari game da tabarbarewar tsaro a Najeriya

Jama’tu Nasril Islam ta koka ga Buhari game da tabarbarewar tsaro a Najeriya

Hadaddiyar kungiyar Musulman Najeriya dake karkashin jagorancin Sarakunan gargajiya Musulmai, Jama’tu Nasril Islam ta koka kan yadda lamarin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya dama sauran sassan Najeriya gaba daya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sakataren JNI, Sheikh Khalid Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu, inda yace akwai bukatar shuwagabanni a dukkanin matakai su dage wajen yunkurawa domin share ma jama’ansu hawaye.

KU KARANTA: Ka fuskanci matsalar tsaro a Kaduna ka rabu da shuwagabannin mu – Yarbawa ga El-Rufai

Jama’tu Nasril Islam ta koka ga Buhari game da tabarbarewar tsaro a Najeriya
Sheikh Khalid
Asali: UGC

Khalid yayi kira ga Musulmai dasu dage wajen gudanar da addu’o’I samun tsaro, cigaba mai daurewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da dawwamar hakan a Arewacin Najeriya dama Najeriya gaba daya.

“JNI ta dade tana kira ga Musulmai dasu dage wajen gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da cigaba mai daurewa a Najeriya, a yanzu ma muna sake yin irin wannan kira ga jama’anmu, musamman duba da yadda lamarin tsaro ya tabarbare, satar mutane, kashe kashe da talauci na karuwa.

“Don haka muke kira ga shuwagabanni dasu tabbata sun sauke nauyin dake wuyansu domin kuwa jama’a na kokawa a yanzu haka, don haka ya kamata mu dage wajen neman yardarm Allah a duk abinda zamu yi.” Inji shi.

Daga karshe JNI tayi kira ga Musulmai su jajirce wajen gudanar da Ibada a cikin wannan wata mai tsarki ta hanyar yin sallolin farilla guda biyar cikin jam’I da sallar Asham, yawaita karatun Qur’ani, ambaton Allah da kuma tunawa da Allah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel