'Yan zanga-zangar da Atiku ya dauka sun afka cikin kotun da ake sauraron karar zabe

'Yan zanga-zangar da Atiku ya dauka sun afka cikin kotun da ake sauraron karar zabe

- Wasu 'yan zanga-zanga da suke goyon bayan Atiku Abubakar sun shiga cikin harabar kotun da ake sauraron karar zabe a yau suna ta ihu

- 'Yan zanga-zangar wadanda matane zalla kusan guda 40 sun yiwa harabar kotun kawanya

A yau Laraba ne wasu mata a Abuja suka gabatar da wata zanga-zanga akan zargin cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ki bin umarnin kotun daukaka kara dake Abuja, wurin bai wa jam'iyyar PDP da dan takarar ta, Atiku Abubakar, damar binciken kayan da aka gabatar da zabe dasu a ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekarar.

Matan wadanda yawansu ya kai kusan 40, sun gabatar da zanga-zangar ta su ne a cikin harabar kotun daukaka kara da ke Abuja, a lokacin da ake sauraron karar zabe da aka gabatar a yau Larabar nan.

'Yan zanga-zangar da Atiku ya dauka sun afka cikin kotun da ake sauraron karar zabe

'Yan zanga-zangar da Atiku ya dauka sun afka cikin kotun da ake sauraron karar zabe
Source: Original

Matan sun cigaba da gabatar da zanga-zangar har sai da aka gama zaman sauraron karar da karfe 1:20 na rana.

Kotun daukaka karar ta bai wa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP damar binciken kayan da aka gabatar da zabe da su na hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

KU KARANTA: Ta faru ta kare: Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa masarautu hudu a jihar Kano

Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ki bin umarnin da kotu ta bayar ranar 7 ga watan Maris.

Masu zanga-zangar suna maganganu suna cewa, "Mutane na mutuwa, bama iya zuwa gonakin mu noma, lauyoyi ku gyara harkar dimokradiyyar kasar nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel