Fati Washa ta samu mabiya Miliyan 1 a shafin Instagram

Fati Washa ta samu mabiya Miliyan 1 a shafin Instagram

Fitacciyar jarumar wasan kwaikwayo a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta dandalin Kannywood, Fati Washa, ta yi gagarumar bajinta ta shahara da dumbin masoya inda ta samu mabiya fiye da miliyan daya a shafin zauren sada zumunta na Instagram.

Fati Washa
Fati Washa
Asali: Getty Images

Bayan sanya sakonni da hotuna kimanin 710 a shafin ta na zauren sada zumunta, Fati Washa ta samu masoya fiye da miliyan daya da ke bibiyar ta a dandalin sada zumunta na Instagram.

Domin bayyana murna gami da farin cikin ta, fitacciyar jarumar ta aike da sakon godiya ga masoya a sanadiyar gagarumar gudunmuwa da su ka bayar a wannan mataki da ta kai na mashahuranci a dandalin sada zumunta.

KARANTA KUMA: 2023: Ku manta da burin kujerar shugaban kasa, ku samar da aiki ga Matasan ku

Jaruma Fati Washa mai bin mutane 580 kacal a shafin ta na Instagram, ta rubuta wani sako na karamci da bayyana tsagwaran soyayyar mabiyan ta da ta mammaye zuciyar ta a halin yanzu. Ta taya su murna da mika gaisuwar watan Azumin Ramalana a gare su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel