Ban kamu da kowani ciwon zuciya ba - Abokin takarar Atiku, Peter Obi

Ban kamu da kowani ciwon zuciya ba - Abokin takarar Atiku, Peter Obi

Tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi, ya caccaki ikirarin cewa yayi fama da ciwon zuciya.

A wani jawabi daga hadiminsa, Valatine Obienyem a ranar Talata, 7 ga watan Mayu ya bayyana yadda Obi yayi fama da zazzabi sannan ya ziyarci asibitin Onitsha, inda ya ga likita sannan aka masa gwaje-gwaje.

Obienyem ya kuma bayyana yadda Obi ya koma gida, sannan ya shirya ya tafi aiki a wannan rana.

Sai dai da yake martani akan batun cewa Obi na fama da ciwon zuciya, Obienyem yayi watsi da ikirarin, inda ya bayyana cewa Obi na cikin koshin lafiya kuma bai yi kowani ciwo da ya shafi zuciya ba kamar yadda wasu mutane suka yi ikirari.

Ban kamu da kowani ciwon zuciya ba - Abokin takarar Atiku, Peter Obi
Ban kamu da kowani ciwon zuciya ba - Abokin takarar Atiku, Peter Obi
Asali: UGC

Kalamansa: “Jiya, na wallafa wani rahoto kan yadda tsohon gwamnan jihar Anambra yayi fama da zazzabi sannan ya ziyarci asibitin Onitsha. Na kuma rahoto cewa kai tsaye ya tafi ofishinsa don ci gaba da aiki. Mun shafe dukka ranar wajen shirya yadda zai mayar da hankali ga aikinsa na gaba: bayar da tallafi ga zababbun asibitoci 50.

KU KARANTA KUMA: Buhari da APC ne ya kamata su dauki alhakin rashin tsaro – Atiku

“Kawai sai aka wayi ari an sauya rahoton cewa Obi na fama da ciwon zuciya. Nayi imani duk wanda ya kirkiro wannan mugun alkaba’i da karya daidai yake da yi masa fatan mutuwa. Amma ba da jimawa ba zai gane cewa Allah ne ke rike da duk abun halitta, hakan zai fi masa.

“Zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana cewa Obi bai yi fama da ciwon zuciya ba kuma yana cikin koshin lafiya.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: